logo

HAUSA

Wang Yi: Sin na fatan hade dabarun raya kasa da Jamaica

2024-01-21 15:18:59 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana cewa, kasarsa tana fatan yin hadin gwiwa da kasar Jamaica, wajen daidaita dabarun raya kasa, da kara yin hadin gwiwa a fannoni daban daban, da inganta mu'amala tsakanin al’ummomi da musayar al'adu, da karfafa tushen ra'ayin jama'a, a wani mataki na sada zumunta tsakanin Sin da Jamaica.

Wang, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya bayyana hakan ne a wata ganawa da firaministan Jamaica Andrew Holness, ganawar da ta samu halartar ministocin harkokin waje, kudi, kiwon lafiya da kayayyakin more rayuwa na kasar Jamaica.

A jawabinsa Holness ya tunatar cewa, a shekarar 2009, ya samu damar tarbar shugaba Xi Jinping, wanda ya ziyarci kasar Jamaica a matsayin mataimakin shugaban kasar Sin, kuma a shekarar 2019, shi da shugaba Xi sun bayyana hadin gwiwa tare da inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa manyan tsare-tsare.

Ya kuma bukaci Wang ya mika sakon gaisuwarsa ga shugaba Xi, yana mai cewa, kasar Sin ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen taimakawa kasar Jamaica yayin da ta fuskanci matsaloli, wanda ya taimakawa bunkasuwar tattalin arzikin Jamaica da inganta rayuwar jama'ar kasar, kuma ya nuna a fili cewa, kasar Sin na son taimakawa kasashe masu tasowa.

Firaministan ya jaddada cewa, Jamaica za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan manufar Sin daya tak a duniya, da ba da fifiko kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da kokarin kulla kawance mai karfi bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu. (Ibrahim)