logo

HAUSA

WEF ya yi kira da a sake karfafa amana domin fuskantar kalubale

2024-01-20 16:44:44 CMG Hausa

An kammala taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya wato WEF a takaice na shekarar 2024 da aka shafe kwanaki 5 ana yinsa a birnin Davos na kasar Switzerland a jiya Jumma’a ranar 19 ga wata, inda mahalarta taron da dama suka yi kira da a karfafa yin riko da amana da hada kai don magance kalubalen da ake fuskanta na rashin tabbas a duniya.

Shugaban dandalin WEF, Borge Brende, ya gabatar da jawabi a wajen rufe taron, inda ya ce duniya na fuskantar kalubale masu tsanani da sarkakiya, kuma hadin gwiwa don tinkarar wadannan kalubale ya dogara ne kan amana.

Brende ya bayyana cewa, a yayin wannan taron na shekara-shekara, an samu ci gaba a fannonin da suka hada da sauyin yanayi, daidaiton jinsi, bunkasa fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam, da yin gyare-gyare kan tsarin makamashi da dai sauransu. A cikin yanayin da ake ciki na kara samun rarrabuwar kawuna da karkatar ra'ayi, taron na bana ya ba da gudummawa ga inganta tattaunawa, hadin gwiwa, da dangantakar abokantaka a aikace a matsayin babbar hanya ta ciyar da abubuwa gaba.

A nasa bangaren, Klaus Schwab, wanda ya kafa kuma shugaban zartarwa na WEF, ya bayyana cewa, dole ne a farfado da riko da amana a nan gaba, da aminci da karfin shawo kan kalubale, kuma abu mafi mahimmanci shi ne, nuna amincewa da juna, a cewarsa, amincewa shi ne alkawarin da aka dauka kan aiki, imani da kuma fata. (Mai fassara: Bilkisu Xin)