logo

HAUSA

Koriya ta Arewa ta yi gwajin makaman nukiliya da ake harba daga karkashin ruwa

2024-01-19 11:15:48 CMG Hausa

Kamfanin dillancin labarai na Koriya ta Arewa, ya ba da rahoto Jumma’ar nan cewa, kasar ta gudanar da wani gwajin makamin nukiliya da ake harba daga karkashin ruwa.

Rahoton ya bayyana cewa, gwajin ya kasance wani martani ne ga atisayen soja na hadin gwiwa da kasashen Koriya ta Kudu da Amurka da Japan suka gudanar. (Ibrahim).