logo

HAUSA

Isra’ila za ta ci gaba da daukar matakan soja don kame yankin yammacin kogin Jordan

2024-01-19 11:32:21 CMG Hausa

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana a jiya cewa, Isra’ila za ta ci gaba da daukar matakan soja don kwace iko da yankin yammacin kogin Jordan, idan har ana da shirin warware rikicin dake tsakanin Palesdinu da Isra’ila a nan gaba.

Netanyahu ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka gudanar a birnin Tel Aviv a wannan rana da dare cewa, Isra’ila za ta ci gaba da daukar matakan soja a zirin Gaza, har sai an cimma dukkan burin da aka sanya a gaba, wato sakin ’yan Isra’ila da aka yi garkuwa da su, da murkushe kungiyar Hamas da tabbatar da zirin Gaza ya daina zama barazana ga Isra’ila. Ya kuma bayyana cewa, bayan kawo karshen rikicin, tilas ne a dauki matakai da ba na soja ba a zirin Gaza, da tabbatar da sanya yankin Gaza karkashin tsaron Isra’ila.

Rahotanni na cewa, tun a daren ranar 17 ga wata ne, sojojin Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare a yankunan Khan Younis da Rafah da ke kudancin zirin Gaza, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane a kalla 46. (Zainab Zhang)