logo

HAUSA

Mahalartan WEF: Sin muhimmiyar injin hadin gwiwar kasa da kasa

2024-01-19 11:20:27 CMG HAUSA

 

Yanzu haka ana gudanar da taron dandalin tattaunaunawa kan tattalin arzikin duniya (WEF) na shekarar 2024 a garin Davos dake Switzerland.  Mahalarta taron sun bayyana farin ciki kan yadda kasar Sin ta ba da shawarar bude kofa ga kasashen waje. Suna fatan kasar Sin za ta inganta hadin gwiwar kasa da kasa da yadda ake tafiyar da harkokin duniya tare da taka rawar a zo a gani sosai a cikin wannan tsari.

Rahoton da WEF ta fitar mai taken “Hadarin da za a fuskanta a duniya a 2024” ya yi gargadi cewa, rashin isasshen hadin gwiwa tsakanin kasashe kan batutuwan da suka shafi duniya, na iya haifar da dadewa da tabarbarewar rikice-rikice.

Darektan gudanarwa na dandalin, Mirek Dusek ya gayawa wakilin CMG cewa, kasar Sin ta isar da sakon bude kofa da yin hadin gwiwa da juna a yayin taron na bana, kuma mahalarta taron sun yaba matuka da hakan, suna kuma fatan karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da kasar Sin.

Shugaban kamfanin ba da shawara kan hulda da jama'a na Edelman, Richard Edelman ya bayyana cewa, kasar Sin ta taka rawar gani wajen inganta hadin gwiwar kasa da kasa, kuma ba za a iya raba kasar Sin da magance dimbin kalubalen da duniya ke fuskanta kamar tsarin sauya amfani da makamashi da matsalar sauyin yanayi ba. (Amina Xu)