logo

HAUSA

Sin da Kamaru sun yi alkawarin kara samun sabbin nasarori a hadin gwiwar dake tsakaninsu

2024-01-19 09:53:19 CMG Hausa

Mataimakin firaministan kasar Sin Liu Guozhong, wanda ya jagoranci tawagar gwamnatin kasar Sin, ya ziyarci kasar Kamaru daga ranakun Laraba zuwa jiya Alhamis, inda ya gana da shugaban kasar da firaministan kasar, kuma sassan biyu sun lashi takwabin ci gaba da inganta hadin gwiwa a fannoni daban daban.

Liu ya bayyana aniyar kasar Sin ta zurfafa amincewa da juna a fannin siyasa da kasar Kamaru, da karfafa hadin gwiwa da dabarun raya kasa, da tsayawa tsayin daka kan samun moriyar juna da ciyar da hadin gwiwa a tsakaninsu a fannoni daban daban.

Ya kara da cewa, a shirye kasar take ta hada kai da Kamaru a harkokin kasa da kasa, da inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, da ma kiyaye moriyar kasashe masu tasowa, da ba da gudummawa wajen gina babban al'ummar kasashen Sin da Afirka mai makomar bai daya.

A nasa bangare shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya bayyana cewa, kasar Sin babbar kawar Kamaru ce, ya kuma godewa kasar Sin bisa goyon baya da taimakon raya harkoki da take bayarwa a fannoni daban daban. Yana mai cewa, Kamaru tana martaba ka'idar Sin daya tak a duniya, kuma ba za ta sauya manufofi da matsayinta a wannan fanni ba.

Shi kuwa Firaminista Dion Ngute Joseph ya bayyana cewa, kasashen biyu na da dadadden tarihi na abokantaka da hadin gwiwa. Ya kuma bayyana aniyar Kamaru na kara zurfafa hadin gwiwa da kasar Sin a fannonin siyasa, da tattalin arziki da cinikayya, da samar da ababen more rayuwa, da al'adu, da yawon bude ido da harkokin kasa da kasa, ta yadda za a kara samar da alheri ga jama'ar kasashen biyu, da sa kaimi ga samun sabbin nasarori a fannin raya alakar dake tsakanin kasashen biyu.(Ibrahim)