logo

HAUSA

'Yan tawayen Houthi na Yemen sun dauki alhakin kai wani sabon harin makami mai linzami kan jirgin ruwan Amurka

2024-01-19 10:10:37 CMG Hausa

Kungiyar Houthi ta Yemen, ta dauki alhakin kai harin makami mai linzami kan wani jirgin ruwan Amurka a mashigin tekun Aden.

Mai magana da yawun dakarun Houthi, Yahya Sarea ya bayyana a cikin wata sanarwa da tashar talabijin ta al-Masirah ta Houthi ta watsa cewa, sojojin ruwa na dakarun Houthi, sun kai wani hari kan wani jirgin ruwan Amurka mai suna Chem Ranger, a mashigin tekun Aden, inda suka yi amfani da wasu makamai masu linzami da ake harbawa daga jiragen ruwa na yaki, kuma harin ya sauka a inda aka tsara. (Ibrahim)