logo

HAUSA

Ziyarar Ministan Wajen Sin A Afirka: Zumunci Mai Dadi Ba Irin Na 'Yan Ta-more Ba

2024-01-19 19:10:22 CMG Hausa

 daga Abdulrazaq Yahuza


Ziyarar ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, a wasu kasashen Afirka a farkon 2024 kusan al'ada ce da ministocin harkokin wajen kasar kan yi a farkon kowace shekara cikin shekaru 34 a jere.

Irin wannan ziyara da kasar Sin ke yi a farkon shekara tun daga 1991 ta haifar da da mai ido ga Afirka idan aka yi la'akari da yadda aka raya zumuncin aiki da cin gajiyar juna tare da fuskantar kalubalen siyasar duniya domin a gudu tare a tsira tare.

Duk dan Afirka da ya samu wayewar zamani, har yau mulkin mallakar da Turawan yamma suka yi wa Afirka yana masa daci a rai saboda bautarwa da azabtarwa da kakanninmu suka sha a hannunsu. Wannan ya sa duk lokacin da na yi la'akari da huldar kasuwancin da ke tsakanin Afirka da Sin da sauran harkoki sai na kara fahimtar hujjojin kasashenmu na rungumar Sin.

Ziyarar minista Wang Yi, ta karfafa neman goyon bayan Afirka a kan kudurin Sin na kawo ci gaba ga juna a duniya, da tabbatar da 'yanci da tsaro da kuma wayewar kai ta bai-daya da za ta kawo alheri ga kowa da kowa. Irin yanayin da duniya ke ciki yanzu hatta jaririn da ba a haifa ba ya san akwai matsala saboda rashin mutunta hakkin bil'adama da yaudara da rashin mutunta kasashe masu tasowa daga Turawan yamma masu da'awar jagorancin duniya. Abin da Isra'ila ke yi bisa goyon bayan Amurka a yankin Gaza ya nuna hakan baro-baro a fili.

Don haka, Afirka ta yi ma kanta kiyamullaili ta rungumi hulda da Sin domin samun ci gaba. Abin jinjina ne yadda kasashen Afirka 52 suka rattaba hannu a kan yarjeniyoyin tsarin Ziri Daya da Hanya Daya na biliyoyin daloli don samar wa kansu da ababen more rayuwa kamar titunan mota, layukan jirgin kasa, tashoshin teku da sauran abubuwan da ake bukata na bunkasa tattalin arzikin.

A lokacin da minista Wang Yi ya isa kasar Masar, ya nuna cewa kasar Sin tana goyon bayan adalci ga kowa a duniya musamman kan yakin zirin Gaza wanda ya fara fantsama tare da kai hari a kan jiragen ruwa a tekun Bahar Maliya.

A tattaunawarsa da shugaban Tunisiya Kais Saied, Wang Yi ya bayyana yadda kyakkawar alaka ta dore a tsakanin kasashen biyu na tsawon shekara 60 tare da jaddada ci gaba da kawance ta fannonin raya kasa da bunkasar tattalin arziki. Shugaban Tunisiya a nasa bangaren ya jaddada goyon kasar Sin a matsayin kasa daya dunkulalliya tare da yabawa da irin nasarorin da take samu ta fuskar ci gaban zamani.

A kasar Togo, minista Wang Yi ya samu kyakkyawar tarba daga takwaransa na kasar, Robert Dussey inda kasar ta Togo ta sake nanata goyon baya ga Sin musamman kan ci gaba da zaman yankin Taiwan a cikinta. Tana mai cewa kasar Sin kwaya daya ce kwallin kwal a duniya.

A kasar Cote d'Ivoire kuwa inda minista Wang Yi ya yada zango na karshe a ziyarar tasa, ya samu tabbaci daga shugaban kasar, Alassane Ouattara cewa ya yi, kasarsa ba ta da babbar kawa ta cinikayya da zuba jari kamar Sin, don haka za ta ci gaba da kyautata zumuncin da ke tsakaninsu. Abin alfahari ba ga Cote d'Ivoire ba kawai har da sauran kasashen Afirka, minista Wang ya ce Sin za ta ci gaba da inganta tsarin cin moriyar juna da Afirka da kuma taimakon kasashen yankin wajen aiki da tsare-tsare mafi kyau da suka fi dacewa da su ta yadda za su ci gajiyar albarkatun da suke da su yadda ya kamata.

Wannan ziyara da minista Wang Yi ya kawo Afirka, ta sake bai wa yankin damar ci gaba da kulla alakar cinikayya mai gwabi a tsakaninsu. Yana da matukar karfafa gwiwa ga kasashen Afirka bisa yadda Sin take samun bunkasar tattalin arziki. Alkaluman da aka fitar na shekarar 2023 sun nuna hada-hadar tattalin arzikinta sun haura fiye da Yuan tiriliyan 126, da ke nufin ta samu ci gaba da kashi 5.2 cikin dari a kan wanda ta samu a shekarar 2022.

Irin wannan ziyara ta ministan wajen Sin, za ta kara bude hanyoyin da Afirka za ta bi sawun Sin ta fannin kere-kere da kirkire-kirkire da zamanantar da kasashensu.

A wata ziyara da na kai shalkwatar Kamfanin China Harbour Engineering Company da ke Nijeriya a Unguwar Maitama, Abuja a wannan Alhamis din, Manajan Daraktan Kamfanin a Nijeriya, Mista Jason Wang ya bayyana min yadda suka kammala aikin titin Keffi (a Jihar Nasarawa) zuwa Makurdi (a Jihar Benue) da kuma kokarin da suke yi na karasa kashi na biyu na aikin wanda zai hade Makurdi da Enugu. Haka nan mun yi magana a kan tashar tekun da kamfaninsu ya samar a Legas ta Lekki wacce za ta samar da dubban aikin yi da biliyoyin kudin shiga ga Nijeriya.

Duk irin wadannan kyawawan abubuwa sun faru ne sakamakon martaba juna a tsakanin Sin da Afirka, ba kamar Turawan yamma da suka zama 'yan ta-more ba.