Kasar Sin ta harba kumbon dakon kaya domin aikewa da kayayyaki ga tashar sararin samaniya
2024-01-18 21:22:25 CMG Hausa
Hukumar kula da sararin samaniya ta kasar Sin(CMSA) ta sanar da cewa, a daren Larabar nan ne kasar Sin ta harba kumbon Tianzhou-7 da ke dakon kaya, kuma ya kammala daidaitawa, tare da hadewa da tashar binciken sararin samaniya ta Tiangong.