Guterres ya bukaci a tsagaita wuta a Gaza
2024-01-18 13:21:04 CMG Hausa
Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya jaddada yin kira da a tsagaita bude wuta bisa dalilai na jin kai a zirin Gaza, da muhimmancin kafa kasashe biyu domin kawo karshen batun Falasdinu da Isra'ila.
Da yake jawabi a taron tattalin arzikin duniya dake gudana a birnin Davos, Guterres ya bayyana cewa, kasashen duniya ba su dauki mataki ba, yana mai cewa, galibi ana kashe mata da kananan yara, ana raunata su, ana kai musu hare-hare, ana tilasta musu barin gidajensu da hana kai musu kayan agaji.
Ya bayyana cewa, shekarar 2023 da ta gabata, shekara ce da aka fi fama da fari da ambaliya da sauran bala'o'i da suka addabi kasashe da al'ummomi, don haka, wajibi ne a hanzarta daukar matakin don tabbatar da sauyawa ga amfani da makamashi da ake iya sabuntawa bisa daidaito. (Ibrahim)