AFCON 2023: ‘Yan Wasan Da Za Su Haskaka A Gasar Kofin Afirka
2024-01-18 16:12:33 CMG HAUSA
AFCON 2023: ‘Yan Wasan Da Za Su Haskaka A Gasar Kofin Afirka
Kamar yadda aka tsara, a 13 ga watan Janairu aka fara gasar cin kofin Afirka karo na 34, kuma za a kammala ranar 11 ga watan Fabrairu a kasar Ibory Coast, wadda itace mai masaukin baki.
Sai dai gasar ta wannan karon za ta samu bakuncin zakakuran ‘yan wasa da tauraruwarsu take haskawa a duniya kuma sun buga wasanni a gasar a shekarun baya kuma har yanzu suna haskawa.
Muhammad Salah (Masar)
Masar ta yi rashin nasarar lashe kofin a hannun Senegal a shekara ta 2022 a Kamaru, sannan Senegal din ta hana Masar zuwa gasar Kofin Duniya da aka yi a kasar Katar a 2022. Dukkan wasannin a bugun fenariti Senegal ta yi nasara – kuma Salah bai buga fenaritin ba a AFCON, wanda shi ne na karshen bugawa, kuma kafin nan Senegal ta lashe kofin saboda ‘yan Masar ba su ci da yawa ba.
Kofin AFCON na bakwai da Masar ta dauka shi ne a shekarar 2010, kuma Salah na fatan taka rawar gani fiye da wadda ya yi a Gabon a 2017 da kuma a Kamru a shekarar 2022.
Salah ya dauki kofuna da yawa a Liberpool, sai dai zai so ya kara cin kwallo bayan shidan da ya zura a raga daga AFCON ukun da ya halarta, sannan yana son ya jagoranci Masar ta lashe gasar.
Kamar yadda yake taka rawar gani a Liberpool, a bana, Salah ne zai ja ragamar kasar a fafatawa da Ghana da Cape Berde da Mozambikue a rukuni na biyu.
Victor Osimhen (Nijeriya)
Dan wasa Bictor Osimhen ne ya lashe gwarzon dan kwallon Afirka na 2023 a bikin da aka yi ranar 11 ga watan Disamba sannan ya zama na farko da ya lashe kyautar daga Nijeriya tun bayan shekara ta 1999.
A shekara 2021 bai samu zuwa gasar ba sakamakon bullar cutar korona da raunin da ya ji, sai dai shin ko wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afirka na bana zai ja ragamar Super Eagles ta lashe kofin na 2024?
Osimhen mai shekara 24 ya zama daya daga fitattun masu cin kwallaye a Turai, wanda ya zama kan gaba a cin kwallaye a SerieA, kuma hakan ya sa Napoli ta lashe kofin a karon farko tun bayan 1990.
Jinya da Osimhen ya yi ya sa Super Eagles ta yi canjaras da Lesotho da kuma Zimbabwe a wasan shiga gasar Kofin Duniya da za a yi a 2026, sannan tsohon dan wasan Lille din yana cikin tawagar Super Eagles a AFCON 2019, amma daga baya aka saka shi a wasan da kasar ta zama ta uku a wasannin.
Nijeriya tana rukunin da ya hada da mai masaukin baki Ibory Coast da Ekuatorial Guinea da Guinea-Bissau a rukunin farko.
Serhou Guirassy (Guinea)
Dan wasan na taka rawar gani a kungiyar kwallon kafa ta Stuttgard ta kasar Jamus, wanda ya ci kwallo 15 a wasanni 10 a gasar Bundesliga kuma dan wasan mai shekara 27, tsohon matashin tawagar Faransa zai buga AFCON a karon farko, bayan da ya fara yi wa Guine wasa a Maris din shekara ta 2022.
Rukuni na uku za a yi wasannin hamayya da ya kunshi mai rike da kofin Senegal da Kamaru, inda Syli National ke ciki da Gambia, wadda karo na biyu kenan da za ta kara a wasannin.
Raunin da ya ji a watan Nuwamba ya kawo masa tsaiko, amma dai Guinea na fatan Guirassy zai sa kwazon da zai kai kasar zagaye na biyu, inda daga nan komai zai iya faruwa.
Mohammed Kudus (Ghana)
Dan wasa Mohammed Kudus ya ci kwallo biyu lokacin da Ghana ta doke South Korea a gasar Kofin Duniya ta 2022 a Katar kuma Ghana za ta ziyarci makwabciyarta Ibory Coast da fatan ba za ta maimaita abin kunya da ta yi a Kamaru ba, inda aka fitar da ita a wasannin rukuni – har da wanda Comoros ta doke ta 3-2.
Ghana tana tangal-tangal a wasa biyu da ta buga a neman shiga gasar kofin duniya da za a yi a 2026, wadda ta kara rashin nasara a hannun Comoros, sannan Kudus ne kan gaba a cin kwallaye da kasar ta samu gurbin zuwa Ibory Coast mai uku a raga, kuma yana taimaka wa West Ham United a wasan da take bugawa tun bayan da ya koma kungiyar da ke buga Premier League a cikin watan Agusta daga Ajad ta Holland.
Bayan da ya ci kwallo biyu a kofin duniya a Katar a 2022, ko dan wasan mai shekara 23 zai ja ragamar kasar ta taka rawar gani a Ibory Coast?
Azzedine Ounahi (Morocco)
Dan wasa Azzedine Ounahi yayi kokari sosai kuma rawar da dan wasan ya taka a gasar kofin duniya a Katar a 2022 a tawagar Morocco da ta kafa tarihin kai wa dab da karshe ta farko a Afirka – hakan ya sa Marseille ta dauki Ounahi.
Sai dai ya sha jinya tun raunin da ya ji a lokacin da yake buga wa tawagar Morocco wasa a watan Maris, bayan wasa bakwai da ya buga wa sabuwar kungiyarsa ta kasar Faransa.
Ounahi mai shekara 23 na aiki tukuru domin ya taka rawar gani a AFCON, koma ya yi fiye da kwazon da ya saka a gasar Kofin Duniya – sai dai dan wasan bai yi wa Morocco karawa biyu a neman shiga Kofin Duniya ba da ta yi a cikin Nuwamba. Kociyan tawagar, Walid Regragui zai so yin amfani da dan wasan da ya bayar da gudunmuwar da suka kai dab da karshe a kofin duniya, yayin da Morocco ke rukuni na shida da ya hada da Jamhurirae Congo da Zambia da kuma Tanzania.
AFCON 2023: Ma Su Masaukin Baki Sun Doke Guinea Bissau Da Ci 2-0
Seko Fofana da Jean-Philippe Krasso ne suka zura kwallo a raga wanda ya taimakawa kasar Cote d’Ivoire mai masaukin baki samun nasara akan Guinea-Bissau da ci 2-0
Kasar Cote d’Voire ta samu nasarar ne a wasan farko da ta buga a gasar ta bana a filin wasa na Alassane Outara da ya cika makil da magoya baya.
Cote d’Ivoire, wacce ke neman lashe kofin a karo na uku bayan nasarar da ta samu a shekarun 1992 da 2015, ta mamaye wasan na tsawon Lokacin ba tareda baiwa kasar Guinea Bissau wata dama ba.
Magoya Bayan Napoli Sun Isa Cote de Voire Domin Mara Wa Osimhen Baya
Wasu magoya bayan kungiyar Napoli da ke buga gasar Serie A sun mamaye Abidjan domin mara wa daya daga cikin nasu, tauraron Super Eagles, Victor Osimhen baya.
Wasu magoya bayan Napoli sun isa Abidjan ta kasar Cote d’Ivoire, domin nuna goyon bayansu ga fitaccen dan wasansu, Victor Osimhen gabanin gasar cin kofin nahiyar Afrika ta 2023 (AFCON).
Wasan farko da Nijeriya za ta buga shi ne wanda za su kara da kasar Equatorial Guinea a ranar Lahadi.
Osimhen ne, zai jagoranci ‘yan wasan gaban Super Eagles yayin da Nijeriya ke neman lashe kofin Afirka karo na hudu a filin wasa na Alassane Ouattara.
Dan wasan na Nijeriya mai shekaru 25 ya taka rawar gani a kakar wasanni biyu da suka gabata, inda ya taimaka wa Napoli ta lashe gasar Seria A ta farko cikin shekaru 30.
Senegal Ta Lallasa Kasar Gambia A Kokarinta Na Kare Kambunta
Mai rike da kofin gasar kasashen Afirka na AFCON, Senegal ta lallasa kasar Gambia a wasanta na farko na gasar ta bana da ake fafatawa a kasar Cote de’Voire.
A minti na hudu dan wasar kasar Senegal Pape Gueye a jefa kwallo a ragar Gambia bayan da mai tsaron raga Baboucar Gaye ya kasa tare kwallon.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Lamine Camara ya jefa kwallaye biyu rigis a ragar Gambia, hakan yasa ta dare na daya a rukunin C da maki uku.