logo

HAUSA

Tinubu: Ilimi shi ne kawai mafita da zai kawo karshen matsalolin garkuwa da mutane a Najeriya

2024-01-18 08:57:40 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi ala wadai da karuwar matsalolin ayyukan garkuwa da mutane da hare-haren ta’addanci a kasar, lamarin da ya bayyana da cewa, tsantsar rashin hankali ne da tsoron Allah.

Ya bayyana hakan ne a fadarsa dake birnin Abuja lokacin da yake karbar bakuncin wakilan kungiyar musulunci ta Jam’iyyatu Ansaridden.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Shugaban ya ce, duk da cewa hukumomin tsaron kasar na bakin kokarinsu wajen shawo kan wannan kalubale, nan kuma ba da dadewa ba gwamnati za ta bijiro da wasu sabbin manufofi da tsare-tsare da za su tabbatar da ganin matasan kasar sun samu ilimi ingantacce.

Ya ce, ilimi dai shi ne maganin matsalolin da suke tayar da hankulan ’yan Najeriya, inda ya ce, babu wani makamin yaki da talauci da ya wuce samar da ilimi ga al’umma. 

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatarwa wakilan kungiyar ta Ansaridden cewa ya kasance shugaban Najeriya ne bisa kyakkyawar niyyar sauya rayuwar al’umma ta hanyar tabbatar da dauwamammen zaman lafiya da wadatuwar arziki a kasa.

“Yana da muhimmancin gaske a gare mu mun bunkasa ilimi muddin dai muna sa ran ci gaban nahiyar Afrika, a sabo da haka ina kira a gare ku ku mayar da hankali wajen yin addu’o’in musamman tare kuma da ilimintar da matasanmu, domin aikin garkuwa da mutane da hare-haren ta’addanci ba hanya ce ta rayuwa ba.”

A jawabinsa jagoran kungiyar ta Jam’iyyatu Ansaridden Sheik Muhammad Lamine Niass karfafa gwiwar shugaban na tarayyar Najeriya ya yi na cigaba da aiwatar da manufofinsa da za su kawo ci gaban kasa, inda ya tabbatar da kudurin kungiyar tasu na ci gaba da yiwa kasa addu’ar samun ci gaba da kwanciyar hankali. (Garba Abdullahi Bagwai)