logo

HAUSA

Shugabar IMF ta ce karuwar GDPn Sin labari ne mai dadi ga duniya

2024-01-18 09:24:41 CMG Hausa

Babbar daraktar asusun lamuni na duniya (IMF) Kristalina Georgieva, ta bayyana cewa, bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin a shekarar 2023, wani albishir ne ga Sin da ma duniya baki daya.

Kristalina Georgieva ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a gefen taron shekara shekara na dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya karo na 54 dake gudana a birnin Davos cewa, tattalin arzikin Sin ya cimma burin da mahukuntan kasar ke fatan cimmawa, wanda ya kai kusan kashi 5 cikin 100, kuma a hakika ya zarce hakan. Wannan albishir ne ga kasar Sin, kuma albishir ne ga Asiya da ma duniya baki daya, saboda kasar Sin tana samar da kashi daya bisa uku na ci gaban tattalin arzikin duniya.

A ranar Larabar da ta gabata ce, hukumar kididdiga ta kasar Sin ta sanar da cewa, GDPn kasar ya karu da kashi 5.2 bisa 100 kan na shekarar da ta gabata, inda ya karu da kudin Sin yuan triliyan 126.06, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 17.71.

A cewarta, gyare-gyare da bude kofa da dunkulewar tattalin arzikin duniya, hanya ce da ta dace da kasar Sin ta ci gaba da aiwatarwa.

A watan Nuwanban bara, asusun na IMF ya daga mizanin hasashen tattalin arzikin kasar Sin na shekarar 2023 zuwa kashi 5.4 daga kashi 5.0 cikin 100, sannan a shekarar 2024 ya daga hasashen zuwa kashi 4.6 daga kashi 4.2 bisa 100, idan aka kwatanta da hasashen da asusun ya fitar game da tattalin arzikin duniya a watan Oktoba. (Ibrahim)