Mutane 2 sun mutu, wasu 3 kuma sun jikkata a Pakistan sanadiyyar harin Iran
2024-01-17 11:17:07 CMG Hausa
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakistan, ta tabbatar a yau Laraba cewa, yara biyu sun mutu, wasu ‘yan mata 3 kuma sun jikkata a kasar, sanadiyyar keta sararin saman kasar da kasar Iran ta yi ba bisa ka’ida ba.
Wata sanarwar da ma’aikatar ta fitar, ta yi Allah wadai da kausasan kalamai kan keta sararin saman kasar da Iran ta yi, tana mai cewa, Iran ta keta cikakken ‘yancin kasar, kana abu ne da ba za a lamunta ba, da ka iya haifar da mummunan sakamako.
Ta kara da cewa, an kuma kira babban jami’in jakadancin Iran a Pakistan, domin ya isar da korafin kasar na keta mata ‘yanci tare da sanar da Iran cewa, dukkan alhakin harin na kanta ita kadai.
Sanarwar ta ruwaito cewa, Pakistan ta kasance mai daukar ta’addanci a matsayin barazana ga dukkan kasashen dake yankin, lamarin dake bukatar hadin gwiwa domin daukar mataki.
A cewar Pakistan, irin wannan mataki da aka dauka bisa radin kai, bai dace da kyakkyawar huldar makwabtaka ba, haka kuma zai iya kawo tsaiko ga amince da tabbaci a tsakaninsu. (Fa’iza Mustapha)