logo

HAUSA

MDD za ta buga hatimi na musamman na dabbar Loong ta kalandar gargajiya ta kasar Sin

2024-01-17 11:03:28 CMG HAUSA

 

Hukumar dake hatimi ta MDD za ta buga hatimi na musamman mai dabbar Loong a ranar 19 ga wata, a birnin New York don murnar zuwan sabuwar shekara ta Loong ta kalandar gargajiya ta kasar Sin.

Hukumar ta fara buga irin wannan hatimi na dabbobi 12 dake alamta shekarun kalandar gargajiya ta kasar Sin ne a watan Mayun shekarar 2010. Ya zuwa shekarar 2021, hukumar ta kammala buga hatimi mai dauke da wadancan dabbobin 12. (Amina Xu)