logo

HAUSA

Bola Tinubu:Har yanzu Muhammadu Buhari ba ya yi masa katsalandan a gwamnati

2024-01-17 09:34:58 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yaba da dattakon tsohon shugaba Muhammadu Buhari ta fuskar kin yin katsalandan a harkokin gwamnatinsa tun bayan da ya mika masa ragamar mulkin Najeriya.

Ya bayyana hakan ne ranar Talata 16 ga wata a birnin Abuja yayin bikin kaddamar da littafi da mashawarcin tsohon shugaban Femi Adesina ya rubuta mai taken “Aiki Tare Da Buhari”.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Littafin wanda ya tabo nasarorin da tsohon shugaban ya cimma a zamanin gwamantinsa daga shekarar 2015 zuwa ta 2023, masana na ciki da wajen Najeriya ne suka nazarci littafin kafin a kai ga wallafa shi.

A jawabinsa, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce, irin wannan halin da tsohon shugaban ya nuna na janye jiki daga shiga al’amuran gwamnati alama ce dake tabbatar da manufofinsa na baiwa kowa cikakkiyar dama domin amfani da basirarsa wajen kawo ci gaba a dukkannin fannoni.

“Tun lokacin da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar ofis a ranar 29 ga watan Mayun 2023, ya gaya min cewa zai koma mahaifarsa Daura da zama, to amma idan ina bukatar ganinsa kofa a bude take, amma dai ba zan taba shishshigi a kan abun da kake yi ba.”

Shugaba Bola Ahmed Tinubu wanda ya yaba da namijin kokarin tsohon shugaba Muhammad Buhari ta fuskar bujiro da wasu mahimman aikace-aikance raya kasa a zamaninsa, wanda yanzu haka wasu daga cikin ayyukan da ake ci gaba da gudanar da su.

Ya yaba matuka bisa kokarin mawallafin wannan littafi wanda yake ciki da kyawawan dabi’un jagorancin al’umma da kishin kasa irin na tsohon shugaban Muhammadu Buhari, inda ma ya kawo shawarar a rinka amfani da littafin a sashen tarihi dake manyan makarantun kasar. (Garba Abdullahi Bagwai)