Kasar Sin abokiyar hulda ce ta dogon lokaci ga kasashen Afirka
2024-01-17 08:18:01 CMG Hausa
Daga ranar 13 zuwa 18 ga watan Janairun shekarar 2024 ne, mamban hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya kai ziyara kasashe 4 na nahiyar Afirka bisa gayyatar da aka yi masa, wato Masar da Tunisiya, da Togo, da Cote D’Ivoire, domin kiyaye al'adar fara ziyartar kasashen nahiyar Afirka a farkon kowace shekara na kusan tsawon shekaru 34 ke nan a jere.
A dukkan kasashen da Wang Yi ya ziyarta, ya kan bayyana adawar kasarsa ta tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashe da aniyar kasar Sin ta taimakawa kaashen nahiyar raya kansa bisa yanayin da suke ciki da aiwatar da sakamakon da aka cimma a yayin taron dandalin FOCAC.
Bugu da kari, Wang Yi ya jaddada manufar kasar Sin ta goyon bayan kasashen a fannin kare cikakken ’yanci, da yankuna da kuma martaba kimarsu, tare da adawa da sanyawa kasashen takunkumi babu gaira babu dalili.
Ko shakka babu, wadannan kalamai na Mr. Wang, sun kara yin nuni ga jajircewar kasar Sin, wajen tabbatar da goyon bayanta ga kawayenta na Afirka a dukkanin fannonin ci gabansu.
Wadannan dalilai ne kuma, suka sanya dukkan masu kishin ci gaban Afirka, ke ganin a yanzu da ma nan gaba, kasashen nahiyar na da tarin alfanu da za su ci gaba da samu, karkashin wannan dangantaka mai dogon tarihi.
Game da zargin da ake yiwa Sin, na danawa kasashen Afirka tarkon bashi kuwa, bangaren Sin ya sha nanata cewa, Sin da nahiyar Afirka na gudanar da hadin gwiwa yadda ya kamata, an kuma kirkiri batun tarkon bashi ne, domin jefa kasashen nahiyar cikin shakku, ta yadda za su dawwama cikin talauci da koma baya.
Don haka a cewarsa, Sin za ta ci gaba da aiki tare da kasashen Afirka, wajen zartas da manufofin inganta rayuwar al’umma, tare da ba da karin gudummawa ga sashen bunkasawa, da zamanantar da masana’antun nahiyar. (Yahaya, Ibrahim/Sanusi Chen)