logo

HAUSA

Yadda za mu fahimci “zabar kasar Sin shi ne zabar dama”

2024-01-17 22:04:11 CMG Hausa

Yau Laraba 17 ga wata ne, gwamnatin kasar Sin ta fitar da alkaluman bunkasar tattalin arzikin kasar na shekara ta 2023, kuma kwarya-kwaryan sakamakon binciken ya shaida cewa, yawan GDPn kasar na shekara ta 2023, ya zarce kudin Sin Yuan tiriliyan 126, wanda ya karu da kaso 5.2 bisa dari, idan aka kwatanta da na shekara ta 2022, kuma saurin karuwar ya zarce na shekara ta 2022, da kaso 2.2 bisa dari. Alkaluman sun shaida cewa, tattalin arzikin kasar Sin na samun bunkasuwa yadda ya kamata.

A shekara ta 2023, tattalin arzikin duniya ya fuskanci koma-baya, kuma an samu barkewar rikice-rikice a wurare da dama. Asusun bada lamuni na duniya IMF ya yi hasashen cewa, saurin karuwar tattalin arzikin duniya a 2023, ya kai kashi 3 bisa dari, kana, kwamitin kungiyar tarayyar Turai EU ya rage hasashen da ya yi wa saurin karuwar tattalin arzikin kasashen dake yankin masu amfani da kudin EURO, zuwa kaso 0.6 bisa dari. Muna iya ganin cewa, saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin na kan gaba a duk fadin duniya.

A halin yanzu, ana gudanar da dandalin Davos, wato dandalin tattauna tattalin arzikin duniya na shekara ta 2024 a kasar Switzerland, inda aka yi kira da a “kara amincewa”. Shugaban dandalin tattauna tattalin arzikin duniya, Borge Brende ya bayyana cewa, a matsayin kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, kasar Sin za ta iya bayar da gudummawa ga kara aminci tsakanin kasa da kasa. To ina dalilin da ya sa aka yarda da kasar Sin haka? Dalilin kuwa shi ne, yadda aka tabbatar da dorewar manufofin kasar Sin, da ci gaba da fadada bude kofa ga kasashen waje, da kuma zamanantar da kasar Sin daga dukkan fannoni, don kasashen duniya za su iya cin gajiya. (Murtala Zhang)