logo

HAUSA

Sin Da Algeria Sun Lashi Takobin Ci Gaba Da Goyon Bayan Juna Da Hadin Gwiwa

2024-01-17 10:36:29 CMG Hausa

Kasashen Sin da Algeria, sun yi alkawarin ci gaba da marawa juna baya kan batutuwan da suka shafi muradunsu, tare da inganta hadin gwiwarsu a fannoni da dama.

Kasashen biyu sun yi wannan alkawari ne yayin ziyarar Liu Guozhong, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kuma mataimakin firaministan kasar, wanda ya gana a mabambantan lokuta da shugaban kasar Algeria Abdelmadjid Tebboune da firaministan kasar Nadir Larbaoui a Algiers, babban birnin kasar.

Yayin da a bana ake cika shekaru 10 da kulla muhimmiyar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Algeria daga dukkan fannoni, Liu Guozhong ya ce, a shirye Sin take ta dauki wannan lokaci a matsayin wata dama ta hada hannu da Algeria wajen ci gaba da marawa juna baya kan batutuwan dake da alaka da muradunsu da inganta musaya da hadin gwiwa karkashin tsarin shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya.

A nasu bangaren, shugaba Tebboune da firaminista Larbaoui, sun ce karfafa hadin gwiwa da Sin wani muhimmin zabi ne ga Algeria, suna alkawarin taka muhimmiyar rawa a hadin gwiwar raya shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya da kara jan hankalin kamfanonin Sin don su zuba jari a kasar da inganta ci gaba cikin hadin gwiwa.

A cewarsu, dangantakar Sin da Algeria ba mai rushewa ba ce, kuma kasashen biyu suna da ra’ayi iri daya kan muhimman batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya. Sun kuma bayyana cewa, a shirye kasarsu take ta hada hannu da Sin wajen daukaka adalci da daidaito a duniya da kuma kare muradun bai daya na kasashe masu tasowa. (Fa’iza Mustapha)