logo

HAUSA

Wakiliyar musamman ta shugaban kasar Sin za ta halarci bikin rantsar da shugaban kasar DR Congo

2024-01-17 19:44:53 CMG Hausa

Shen Yueyue wakiliyar musamman ta shugaban kasar Sin Xi Jinping za ta halarci bikin rantsar da shugaban jamhuriyar Demokuradiyyar Kongo, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta sanar a yau Laraba.

Mao ta ce bisa gayyatar shugaban DRC Félix-Antoine Tshisekedi Tshilombo, Shen wadda kuma ita ce mataimakiyar shugaban kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama’ar kasar Sin, za ta halarci bikin rantsar da shugaba Tshisekedi a Kinshasa babban birnin DRC a ranar 20 ga wata. (Yahaya)