logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen kasar Sin ya yaba da abota da goyon bayan juna da Togo

2024-01-17 19:23:26 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana yayin da yake ganawa da takwaransa na kasar Togo Robert Dussey a jiya Talata cewa, abokai na kwarai suna goyon bayan juna a lokuta masu muhimmanci.

Wang Yi ya bayyana hakan ne yayin da ya isa filin jirgin sama na Lomé-Tokoin, wanda aka fi sani da filin jirgin saman Gnassingbe Eyadéma. Wang ya kai ziyara Togo bisa gayyata bayan kammala ziyararsa a Tunisiya.

Dussey, ya yi tattaki na musamman don tarbar Wang a filin jirgin sama, ya ce Togo na tsayin daka kan ka'idar kasar Sin daya tak, kuma tana goyon bayan matsayin gwamnatin kasar Sin kan batun Taiwan.

Gwamnatin Togo ta jaddada cewa, kasar Sin daya ce kadai a duniya, kuma a bisa doka gwamnatin jamhuriyar jama'ar kasar Sin ita ce gwamnati daya tilo da ke wakiltar kasar Sin baki daya. Dussey ya kara da cewa, Taiwan wani yanki ne da ba za a iya raba shi da kasar Sin ba. Harkokin Taiwan harkokin cikin gida na kasar Sin ne. (Yahaya)