Wani kwale kwale dauke da fasinjoji sama da 100 ya kife a yankin tsakiyar Nijeriya
2024-01-16 20:02:54 CMG Hausa
Wani kwale-kwale dauke da fasinjoji 100 ya kife, a jihar Niger dake arewa maso tsakiyar Nijeriya.
Shugaban hukumar bada agajin gaggawa na Jihar Niger Abdullahi Baba-Arah, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua da safiyar yau cewa, tuni aka kaddamar da ayyukan kai agajin gaggawa.
Ya kara da cewa, zuwa yanzu, ba a samu gawa ko wani da ya tsira ba. Hatsarin ya auku ne jiya Litinin a yankin Borgu na jihar.
A cewarsa, kwale-kwalen na kuma dauke da hatsi da sauran kayayyaki masu daraja a lokacin da hatsarin ya auku, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa wata kasuwa a jihar Kebbi. (Fa’iza Mustapha)