logo

HAUSA

Babban jami’in bada agaji na MDD ya ware kudi don tallafawa ’yan gudun hijira a Sudan ta Kudu

2024-01-16 10:54:43 CMG HAUSA

 

Babban jami’in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya, a jiya Litinin ya ware dalar Amurka miliyan 10 na gaggawa domin taimakawa kimanin mutane 500,000 a Sudan ta Kudu da suka tsere daga yakin Sudan.

Mataimakin babban Sakare-Janar na MDD kuma mai kula da ayyukan agajin gaggawa Martin Griffiths ne ya ware wannan kudin daga asusun bada agajin gaggawa na MDD, a cewar ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD (OCHA).

"Ya zuwa jiya Litinin, kimanin mutane 500,000 ne suka tsallaka zuwa Sudan ta Kudu tun daga tsakiyar watan Afrilu, lokacin da yakin Sudan ya barke," a cewar OCHA. "A cikin watan da ya gabata kadai, sama da mutane 60,000 ne suka isa Sudan ta Kudu, bayan barkewar rikici a birnin Wad Medani da kewaye, birni na biyu mafi girma a Sudan."

Ofishin ya ce ana sa ran karin dubban mutane za su isa Sudan ta Kudu cikin watanni shida masu zuwa.

OCHA ya ce, za a yi amfani da kudin ne wajen gina matsuguni, bayar da tallafin kudi, samar da ruwa, tsaftace muhalli, da kuma tallafawa ci gaba da jigilar sabbin masu shigowa sansanoni masu cunkoso. (Yahaya)