logo

HAUSA

Shugaban kungiyar tarayyar Afirka ya sake nanata yadda samar da kasashe biyu zai kawo karshen rikicin Isra’ila da Falasdinu

2024-01-16 10:24:24 CMG HAUSA

 

A jiya Litinin ne aka bude taro na 47 na kwamitin wakilan dindindin na kungiyar tarayyar Afirka ko AU a birnin Addis Ababa, babban birnin Habasha, kuma shugaban hukumar ta AU Moussa Faki Mahamat ya jaddada shirin samar da kasashe biyu don kawo karshen rikicin Isra’ila da Falasdinu.

Faki ya ce yayin da tasirin rikicin Rasha da Ukraine ke ci gaba da karuwa, ba za a iya misalta irin tsananin da rikicin Isra’la da Falasdinawa ke ci gaba da yi ba, wanda ya haddasa bala’in jin kai da lalata dukiyoyi. 

Ya kara cewa, “Bala’in da rikicin ya haifar ya girgiza lamirin Afirka, kuma ina sake jadadda kiranmu na tsagaita bude wuta don samar da agajin jin kai da kira ga kasashen duniya da a aiwatar da tsarin samar da kasashe biyu don kawo karshen rikicin.”

Da yake magana kan yadda ake ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula Falasdinawa da lalata hanyoyin rayuwarsu, Faki ya tunatar da cewa, rikicin ya kasance abin damuwa ga Afirka sama da shekaru 60.

Ya kuma yi nuni da cewa, ana bukatar samar da mafita mai dorewa domin tabbatar da jituwa a tsakanin bangarorin biyu da baiwa al'ummarsu damar rayuwa cikin kwanciyar hankali da lumana. (Muhammed Yahaya)