Abubakar Dalhatu: Ina son amfani da ilimin da na samu a kasar Sin don amfanawa sauran kasashe
2024-01-16 15:32:47 CMG Hausa
Abubakar Dalhatu, haifaffen Kano ne, wanda a yanzu haka yake karatun digiri na biyu a jami’ar UCAS dake birnin Bejing na kasar Sin.
A zantawarsa da Murtala Zhang, Abubakar ya bayyana abubuwan da suka burge shi a kasar Sin, ciki har da abinci da yanayi da al’adu da sauransu, da yadda yake mu’amala da abokan karatu da malamansa a makaranta.
Malam Abubakar ya kuma bayyana ra’ayinsa kan yanayin karatu a kasar Sin, da burin da yake son cimmawa ta hanyar karo ilimi a nan. (Murtala Zhang)