Gwamnatin Najeriya ta shirya bikin aza furanni domin girmama tsoffin sojojin da suka mutu a fagen fama
2024-01-16 09:23:53 CMG HAUSA
Jiya Litinin 15 ga wata, shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci bikin tunawa da tsoffin sojojin da suka rasu a lokacin da suke tsaka da kare kasa da kuma sauran sojojin da suka yi ritaya daga aiki.
Shi dai wannan biki ana gudanar da shi a Najeriya a duk ranar 15 ga watan Janairu a matsayin wata alama ta girmamawa ga sojojin kasar da suka mutu, da wadanda suke a raye yanzu haka yayin yakin duniya da yakin basasar kasar da sauran ayyukan tabbatar da zaman lafiya na kasa da kasa.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.