Shugaban kasar Tunisiya ya gana da Wang Yi
2024-01-16 10:50:23 CMG Hausa
Jiya Litinin, shugaban kasar Tunisiya Kais Saied ya gana da mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi a birnin Tunis, fadar mulkin kasar Tunisiya.
Da farko, Kais Saied ya bukaci Wang Yi da ya mika sakon gaisuwarsa ga shugaba Xi Jinping, yana mai cewa, ya amince da ra’ayoyin da shugaba Xi ya gabatar game da tafiyar da harkokin kasa, ya kuma yaba wa kasar Sin dangane da babbar nasarar da ta cimma a fannin zamanintar da kasar, haka kuma, ya yaba matuka kan sakamakon da aka cimma cikin shekaru 60 da suka gabata, bisa hadin gwiwa da bunkasuwar dangantaka a tsakanin kasashen biyu. Ya ce, ko da yake, akwai nisa a tsakanin kasar Sin da kasar Tunisiya, amma jama’ar kasashen biyu suna da zumunci mai zurfi a tsakaninsu, kuma kasarsa tana godiya ga kasar Sin bisa goyon bayan da ta dade tana nuna mata, lamarin da ya taimaka wajen raya kasar da kyautata zaman rayuwar al’umma. Ya ce a nan gaba kuma, kasar Tunisiya za ta ci gaba da goyon bayan shawarar “Ziri daya da hanya daya”, da koyon fasahohin kasar Sin wajen zamanintar da kasar Tunisiya bisa yanayin da take ciki. Haka kuma, kasar Tunisiya tana tsayawa tsayin daka wajen martaba manufar “kasar Sin kasa daya tak”, da kuma kudurin MDD mai lamba 2758, domin goyon bayan kasar Sin wajen kula da harkokin kasarta.
A nasa bangare, Wang Yi ya mika sakon gaisuwar shugaban kasar Sin Xi Jinping ga shugaba Saied, ya ce, tun bayan kulla huldar diflomasiyya a tsakanin kasar Sin da kasar Tunisiya shekaru 60 da suka gabata, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta bunkasa yadda ya kamata. Kuma, abu mafi muhimmanci shi ne, bangarori biyu suna girmama juna, da nunawa juna adalci, da karfafa fahimtar juna a tsakaninsu, da kuma habaka hadin gwiwarsu, domin cimma moriyar juna. Kwanan baya, shugabannin kasashen biyu sun zanta ta wayar tarho, inda suka kara daidaita hanyar raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Kasar Sin tana godiya ga kasar Tunisiya, domin irin goyon bayan da ta nuna wa kasar Sin kan manyan batutuwan dake shafar ‘yancin kan kasar Sin, a sa’i daya kuma, kasar Sin tana goyon bayan kasar Tunisiya, wajen kare mulkin kai da ‘yancin kanta, da kuma kiyaye mutuncin al’ummar kasarta, kana, kasar Sin tana goyon bayan kasar Tunisiya wajen neman hanyar bunkasuwa bisa halin da take ciki, da aiwatar da gyare-gyaren raya kasa cikin ‘yanci.
Bugu da kari, shugaba Saied da minista Wang Yi, sun yi musayar ra’ayoyi kan rikicin Isra’ila da Falesdinu. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)