logo

HAUSA

Sin ta riga ta bayar da gudunmawar da ake bukata ga ci gaban tattalin arzikin duniya

2024-01-16 16:40:30 CMG Hausa

An bude taron tattauna tattalin arzikin duniya na shekara-shekara jiya Litinin a garin Davos na Switzerland. Taron na kwanki 5 na bana zai mayar da hankali wajen tattauna wasu batutuwa 4 da suka hada da samar da tsaro da hadin gwiwa da guraben ayyukan yi da amfani da fasahar AI da tsare-tsaren kare muhalli da makamashi a duniya.

Abun nufi, taron zai yi kira ga kasashen duniya da su bayar da gudunmawa a wadannan bangarori. Idan muka nazarci wadannan batutuwa a matsayin masu bibbiyar harkoki da ayyukan kasar Sin, za mu ga cewa, tuni ta riga ta taka rawar gani a wadannan bangarori.

Misali, kasar Sin ta kassance har kullum mai rajin tabbatar da cudanya da mu’amala tsakanin kasa da kasa, inda take adawa da kafa wani dan karamin rukunin ko kuma rarrabuwar kawuna. Akwai wata karin magana ta nahiyar Afrika da Ingilishi dake cewa, “if you want to go fast, go alone. If you want to go far, go together”, wato dai muddan ana son tafiya mai nisa, wanda ke nufin samun nasara mai dorewa to kamata ya yi a tafi tare. A samu cudanya tsakanin bangarori mabanbanta bisa yanayi na adalci da girmama juna kamar yadda kullum Sin take kira da a aiwatar. Idan kuma sauri ake so, to mutum ya tafi shi kadai. Amma Hausawa kan ce, “sauri kan haifi nawa” wato akasari, ba a samu sakamako mai kyau a karshe.

Idan muka tabo batun guraben ayyukan yi kuwa, kasar Sin ta yi suna wajen gudanar da ayyukan more rayuwa a kasashen duniya, musamman kasashe masu tasowa da su ne suka fi fama da matsalar rashin ayyukan yi. Baya ga samar da ci gaba da saukaka rayuwa, wadannan ayyuka suna ci gaba da samar da dimbin guraben ayyukan yi ga mazauna yankuna, ayyuka kuma ba na kai tsaye kadai, har da wadanda ba na kai tsaye ba, lamarin dake kara kudin shiga ga al’umma, da saukaka yanayin rayuwa, a karshe kuma, ya kai ga wanzuwar tsaro da zaman lafiya.

Idan ana batu ne na fasahohin zamanin kamar na AI, to dole ne a sanya kasar Sin a kan gaba saboda gudunmawar take ci gaba da bayarwa a wannan bangare, inda har kullum ake cin moriyar ilimi da fasahohinta a duniya.

Haka ma batun kare muhalli wanda ya zama wani babban kira na shugaban kasar Sin, wato tabbatar da zaman jituwa tsakanin muhalli da halittu, wanda ya kasance batu da ake aiwatarwa a aikace ba fatar baki kadai ba. (Fa'iza Mustapha)