logo

HAUSA

An bude taron Davos na shekarar 2024

2024-01-16 10:55:31 CMG Hausa

Jiya Litinin ne, aka bude taron dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya na shekara-shekara na shekarar 2024 a birnin Davos na kasar Switzerland. A yayin taron mai taken “Farfado da amincewa”, za a mai da hankali kan batutuwan gaggawa na duniya, kamar ci gaban tattalin arzikin duniya, da sauyin yanayi, da sauran batutuwan dake janyo hankulan kasashen duniya, domin karfafa hadin gwiwar dake tsakanin bangarori daban daban.

Wakilai sama da 2800 daga kasashe da yankuna guda 120 sun halarci taron na wannan karo, ciki har da shugabanni da manyan jami’ai daga kasashe kimanin guda 60. A yayin taron na kwanaki 5, ana sa ran wakilai daga bangarori daban daban za su gudanar da taruka da dama, domin tattauna batutuwa masu muhimmanci dake fuskantar ci gaban duniya, inda za su fito da daftarin warware matsalolin da abin ya shafa.

Haka kuma, an gabatar da manyan batutuwa guda 4 da za a tattauna a taron, wadanda suka hada da “Samar da tsaro da hadin gwiwa a duniya mai fama da sauye-sauye” da “Samar da guraben ayyukan yi da karuwar tattalin arziki a sabon zamani” da “Yin amfani da fasahar AI domin inganta bunkasuwar tattalin arziki da zaman takewar al’umma” da “Aiwatar da manyan tsare-tsare domin kare yanayi da muhallin hallitu da makamashi cikin dogon lokaci”. Schwab, wanda ya kafa kuma shugaban zartarwa na dandalin tattalin arziki na duniya, ya bayyana a jajibirin taron shekara-shekara cewa, a yayin da ake fuskantar rarrabuwar kawuna a duniya da zamantakewar al’umma, ya kamata mu daidaita matsalolin dake gabanmu, da gano tushen abubuwan dake faruwa, ta yadda za a gina wata makoma mai haske cikin hadin gwiwa, da farfado da amincewar al’umma kan makomarsu. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)