logo

HAUSA

Za a gyara titunan da suke kan iyakokin dake jihar Borno

2024-01-15 09:47:04 CMG Hausa

Gwamnan jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana takaicin yadda masu manya motocin dakon kaya dake sintiri zuwa kasashen makwaftan jihar ke taka rawa wajen lalacewar hanyar Maiduguri zuwa Gamboru dake yankin karamar hukumar Ngala.

Ya bayyana hakan ne ranar Lahadi 15 ga wata lokacin da ya kai ziyara yankin domin duba halin da hanyar ke ciki. Ya ce, lodin wuce kima da motocin ke yi yana shafar karkon hanyar sosai.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce, babban kuskuren da masu motocin ke yi shi ne dorawa mota kayan da suka wuce tan 100 wadanda suka hadar da siminti da sauran kayan masarufi.

Gwamnan ya ce, gwamnati ta sha gyara hanyar saboda muhimmancinta ga ci gaba kasuwancin tsakanin kasa da kasa, wanda hakan yana taimakawa sosai ga bunkasar tattalin arzikin al’ummar Borno da ma kasa baki daya.

Ya ce, sakamakon yawan lodin da motocin suke yi yanzu haka gadar da ta hade Najeriya da kasashen Kamaru da Chadi tana daf da karyewa.

“Daya daga cikin muhimmin abun da muke bukatar kyautatawa shi ne cinikayya a kan iyakoki, saboda zai kyautata yanayin zamantakewar al’ummar jihar Borno musamman mazauna yankin Gamborun-Gala. Zai rage ayyukan ’yan ta’adda, talauci zai ragu muddin aka samu karuwar cinikayya a tsakanin al’umomin dake kan iyakoki.”

Ya jaddada bukatar tilasta amfani da dokar lodi domin dai kare irin wadannan tituna da kuma rayukan al’umma. (Garba Abdullahi Bagwai)