logo

HAUSA

Deng Chaoyu: ‘Yar kabilar Tujia tana kokarin yada al'adun kabilarta ta hanyar adabi da waka

2024-01-15 14:40:18 CMG Hausa

"Furen da nake da shi, ya bude bayan saukar ruwan sama; kamshinsa ya cika lambun, har malam-bude-littafi ya zo gare shi." wannan wata gajeriyar waka ce da Deng Chaoyu ta rubuta. Deng wata matashiya daga gundumar kabilar Tujia ta Changyang mai cin gashin kanta a Yichang, wani birni a lardin Hubei na tsakiyar kasar Sin. Ta ce wakar tana nuni da cewa, idan mutum ya dage kan abin da yake so, kuma idan ya ba da isasshen lokaci don bunkasa sha'awarsa, ko ba jima ko ba dade, abin zai zama ranarsa, wanda zai zama abin yabawa ga wasu. Deng tana son rubutu da rera waka, kuma ta taimaka wajen zayyana tufafin surfani wadanda ke dauke da kayan adon fasaha na mutanen kabilar Tujia, wadanda aka fi sani da Xilankapu. Ta ba da tata gudunmuwar wajen bunkasa fasaha da al'adun gargajiya na kabilar Tujia.

"Daya, biyu, uku, hudu, biyar, shida, bakwai, takwas ... Wannan ya zama 'danbagou', wato da'ira mai kama da zanen kugiya takwas, wanda shi ne daya daga cikin al'adun gargajiya, da fasahar zane-zane a kayan ado na kabilar Tujia," Deng ta bayyana hakan yayin da take zantawa da manema labarai. Tana rike da tabarmar wuri mai siffar zagaye na kayan teburi. A gidan Deng, yawancin kayan gidanta an yi musu ado da kyallen Tujia, wanda aka fi sani da Xilankapu.  

Xilankapu, wanda ke nufin "zanin gadon saka na fure" a yaren Tujia, an sanya shi a cikin jerin kayayyakin al'adun gargajiya da aka gada daga kakani zuwa kakani na kasar Sin a shekarar 2006. Yana daya daga cikin shahararrun nau’ikan tufafin surfani na kasar Sin. Xilankapu ya sha bambam saboda fasahar sakar hannu da ake amfani da ita wajen yin shi; Zaren siliki mai launuka daban daban, auduga da zaren ulu ana saka su don samar da kayatattun zane a kwance, yayin da zaren auduga masu zurfin launi ana saka su don samar da kayatattun zane a tsaye. Tsarin Xilankapu na gargajiya ya kunshi zanen shimfidar yanayi, tsuntsaye da dabbobi, kayan gida, furanni da sauran tsirrai, zane-zane masu alaka da lissafi, da haruffan Sinanci masu kyawawan ma'ana.

Tunanin farko na Deng game da Xilankapu ya samo asali ne tun lokacin da take karama, lokacin da take gundumar Changyang. Deng ta ce, "a shekaru 5 zuwa 6, na ga mahaifiyata ta ajiye kayayyakin gadonta da kayan kwalliyar takalmi a kan surfanin Xilankapu, daga bisani ta shimfida su a kasa domin kayayyakin su sha iska. Mama ta ce min muhimman sadaki ne ga duk wata 'yar Tujia."  

Tsarin zane-zanen ''danbagou'' na gargajiya yana kama da mutane rike da hannun juna, wanda ke nuna hadin kan al'ummar kasar Sin, in ji Deng. Xilankapu, wata taska ta al'adun ‘yan kabilar Tujia, an gado shi fiye da shekaru 1,000 daga zamani zuwa zamani. Yana ingiza Deng don kara son yanayi da mutunta rayuwa. Tana da yakinin cewa hakkin kiyaye da habaka nau’in fasahar kabilarta ta musamman yana wuyanta.   

A cikin 2017, an gayyaci Deng don halartar taron rufe bikin fina-finai na Cannes wanda ya shahara a duniya, a kasar Faransa. Ta fara fitowa a fagen fina-finan na duniya da jajayen tufafi, dauke da adon zanen tsuntsun Phoenix da surfanin Tujia. "Phoenix wata muhimmiyar abar daraja ce ga ‘yan kabilar Tujia. Lokacin da na tattauna da mai tsara kayana game da tufafi da zan sanya zuwa bikin fina-finan, nan da nan na yi tunanin tufafin Tujia na kabilarmu, amma ina so a yi wani sabon salo a tufafin. Wasu gungun mata masu aikin hannu suka kammala rigata ta 'Jar phoenix' a cikin watanni biyar. Na yi matukar farin ciki da nuna fasahar kabilata ga mahalarta bikin fina-finai din, wadanda suka zo daga sassan duniya," in ji Deng.

Ba abin mamaki ba ne, da rigar Deng ta burge abokai da yawa daga kasashen waje, wadanda suka yaba wa surfanin Tujia a matsayin "kyakkyawa" ko "mai ban sha’awa." Da yawansu sun rungumi Deng sosai. Deng ta gabatar da surfanin Tujia, a matsayin kyauta, ga 'yar wasan Faransa Juliette Binoche da wasu baki. “Ni ‘yar kabilar Tujia ce, na taso ne da tasirin al’adu da fasahar Tujia, duk inda na je ba zan taba mantawa da inda ‘tushena’ yake ba, ina fatan in nuna kwarjinin kabilata ga duniya. Ina alfahari da kasancewa ‘yar kasar Sin, kuma, musamman, ina alfahari da kasancewata 'yar kabilar Tujia," in ji Deng, a yayin bikin.

Deng tana son rubutu da rera waka. Lokacin da aka tambaye ta game da wakarta mai taken Furanni Da Malam-bude-littafi, Deng ta bayyana cewa, "Na rubuta ta lokacin da nake jami'a. Wasu daga cikin abokan karatuna sun nakalto wakar lokacin da suke soyayya da budurwansu. Amma, a gaskiya, ina so in bayyana muhimmancin dagewa a cikin wannan waka. Tohon fure yana jira, jira sosai, har sai damina ta zo, kuma fure ta bude, kamshinsa zai jawo hankalin malam bude littafi. Haka mu ma mutane. Idan muka girma cikin koshin lafiya da tabbaci, sai mu zama kamar furanni masu kamshi, kuma za mu sami amincewa da godiya daga wasu."

A cikin 'yan shekarun nan, Deng ta rubuta wakoki da rera wakoki game da garinsu Changyang. Sanye da tufafin Tujia da ta fi so, mawakiyar matashiya ta yi wasa a shirye-shirye daban-daban da gidan talabijin na kasar Sin (CCTV) ya shirya. "Muhimmin salo na wake-wake na kasa shi ne gadon ayyukan gargajiya. Watakila nan da shekaru biyar, ko kuma shekaru 10, zan iya rera karin wakokin da ke nuna fasahar surfaninmu ta Tuijia da kuma sauran kyawawan al'adun kabilarmu," a cewar Deng.

Wata mata 'yar kabilar Tujia da ake yi wa lakabi da Aping tana sha'awar waka. Lokacin da Aping ke yarinya, ta yi mafarkin zama malamar kida. A ranar 3 ga Satumba, 2020, tare da hadin gwiwar gidauniyar kula da zamatakewar jama'a ta kasar Sin, Deng ta kaddamar da wani shiri na taimakawa 'yan kabilar Tujia wajen cimma burinsu a fannin waka. Aping ce ta ci gajiyar wannan aikin. Ta samu tallafin kudi don yin karatu a makarantar da ke da kyawawan kayan koyan waka. Kawo Yanzu, Aping tana kan hanyarta na cimma burinta.

Deng ta kuma gudanar da wani shagali na ba da tallafi a birnin Yichang. Ta tattara kudade, wanda ta ba wa iyalan Tujia marasa galihu, domin ‘ya’yan iyalan su samu damar zuwa makaranta. Ta kuma samar da kudade don gina dakunan koyon waka da kida da dakunan karatu a Changyang. Deng tana fatan 'yan kabilar Tujia da yawa za su shiga ajujuwa, don samun ingantaccen ilimi. Ta kuma yi fatan yaran za su gaji al'adunsu da fasahar kabilarsu.

Masu sauraro, da haka muka kawo karshen shirinmu na yau na In Ba Ku Ba Gida, da fatan kun ji dadinsa. Tare da wannan waka mai nishadantarwa, a madadin Mohammad Baba Yahaya da ya fassara bayanin, ni Kande da na shirya muku shirin nake cewa a kasance lafiya daga birnin Beijing.(Kande Gao)