logo

HAUSA

Yadda aikin gine-gine na kasar Sin suka taimaka wajen gudanar da gasar cin kofin Afirka

2024-01-15 00:02:46 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

A jiya Asabar ne aka kaddamar da gasar cin kofin nahiyar Afrika karo na 34 a Abidjan, babban birnin harkokin tattalin arziki na kasar Cote d’Ivore, inda kuma aka gudanar da wasan farko na gasar a filin wasa na Alassane Ouattara dake birnin na Abidjan, filin wasan da kasar Sin ta ba da gudummawar ginawa.

Za a shafe kusan wata guda ana fafatawa a gasar wadda za ta gudana a filayen wasa 6 dake birane 5 na Cote d’Ivore, kuma kamfanonin kasar Sin ne suka gina wasu daga cikin filayen wasan da suka hada da na Korhogo da na San Pedro, wato baya ga filin wasa na Alassane Ouattara.

Daidai kwanaki biyu kafin bude gasar kuma, aka bude wata gada da kamfanin gine-gine na kasar Sin ya gina, wadda za ta rage cunkoso a titunan Abidjan, yayin da dubban dubatar masoya kwallon kafa daga sassan duniya ke zuwa kasar domin halartar gasar cin kofin nahiyar Afirka karo na 34. A ranar 10 ga wata, firaministan kasar Cote d’Ivoire Robert Beugre Mambe ya duba ingancin gadar, inda ya bayyana aikin gadar a matsayin wani muhimmin shiri na samar da ababen more rayuwa, wanda ya zama muhimmiyar hanyar sufuri don kyautata zirga-zirga a babban birnin kasar Abidjan.

Hakika, filayen wasa da kuma gada da kasar Sin ta gina a kasar Cote d’Ivoire, wani bangare ne kadai na yadda kasar Sin ke taimakawa wajen gina manyan ababen more rayuwa a kasashen Afirka. Amma mene ne dalilin ta na yin haka? Sabo da kasancewar Sin kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kuma Afirka nahiya ce da aka fi samun kasashe masu tasowa, ban da dankon zumunci da ke tsakaninsu, suna kuma fahimtar juna. Sakamakon yadda kasar Sin ta san muhimmancin ababen more rayuwa ta fannin ci gaban kasa, shi ya sa take iya kokarin aiwatar da hadin gwiwa da kasashen Afirka ta hanyoyi daban daban, don inganta ababen more rayuwa a kasashen, da ma kwarewarsu wajen raya kansu da tabbatar da dauwamammen ci gaba. Bisa ga tsarin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, kawo yanzu kamfanonin kasar Sin sun gina layukan dogo a Afirka da tsawonsu ya zarce kilomita dubu 10, baya ga hanyoyin mota da suka kai kusan kilomita dubu 100, da gadoji kusan dubu da tashoshin jiragen ruwa kusan dari, da ma dimbin asibitoci da makarantu da filayen wasa.

Na san da yawa daga cikinku masu sha’awar wasan kwallon kafa ne, to me zai hana ku je wajen gasar cin kofin Afirka da ke gudana a Cote d’Ivoire? Ina da imanin gada da ma filayen wasan da kasar Sin ta gina za su kara sa ku jin dadin gasar. (Mai Zane:Mustapha Bulama)