logo

HAUSA

Zambiya ta sanar da karin matakan magance cutar kwalara

2024-01-15 11:34:52 CMG Hausa

Kasar Zambiya ta sanar da daukar tsauraran matakai da nufin dakile barkewar cutar kwalara a sassan kasar.

Ministar lafiya ta kasar Sylvia Masebo ta ce, gwamnati ta gabatar da wani tsari a cikin matakan da aka sanar tun da farko, don inganta matakan rigakafin cutar.

Ta shaida wa taron manema labarai da aka shirya domin yin karin haske game da matakan yaki da cutar cewa, tsarin da aka gabatar ya kuma haramta shigar da gidajen kwanciya a cikin cibiyoyin yaki da cutar da kuma binne wadanda ake zargi cutar kwalara ce ta halaka su.

Sauran matakan da aka dauka a baya, sun hada da takaita cinikin abinci a yanayi na rashin tsafta, da haramta taron jana'iza ga mutanen da suka mutu sakamakon cutar, yayin da aka ba wa majami'u damar haduwa na tsawon sa'o'i biyu kawai.

Ta kara da cewa, har yanzu adadin wadanda suka kamu da cutar na da yawa sosai. Ko da yake ana ci gaba da yakar cutar ta bangarori daban-daban.

Bayanai na nuna cewa, an sami sabbin wadanda suka kamu da cutar da suka kai 431, sai mutane 11 da cutar ta halaka cikin sa'o'i 24 da suka gabata a cikin larduna shida daga cikin 10 na kasar, yayin da aka sallami mutane 388 da suka yi fama da cutar daga asibiti. (Ibrahim)