logo

HAUSA

Wang Yi ya bayyana sabon kwalejin da Sin ta gina a Tunisia a matsayin sabuwar alama ta zumunta

2024-01-15 21:45:29 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana sabon kwalejin nazarin harkokin diflomasiyyar kasa da kasa na Tunis da aka kaddamar a yau Litinin, wato kwaleji daya tilo na harkokin diflomasiyya da Sin ta taimaka wajen ginawa a wata kasar Larabawa, a matsayin sabuwar alama ta dankon zumunta, kuma dandalin raya abotar Sin da Tunisia.

Wang Yi wanda kuma mamba ne a ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya bayyana haka ne yau, lokacin da yake jawabi yayin bikin bude kwalejin a birnin Tunis. Bikin ya samu halartar shugaban kasar, Kais Saied da ministan harkokin wajen kasar, Nabil Ammar.

Wang Yi ya kuma yi kira da a yi kokarin inganta gina tsarin duniya mai daidaito tsakanin kasashen duniya da dama da dunkulewar tattalin arzikin duniya domin kowa ya amfana. (Fa’iza Mustapha)