logo

HAUSA

Gidauniyar Bill da Melinda Gates ta yi kira ga kasashen duniya da su yi kokarin rage yawan mutuwar iyaye mata da jarirai

2024-01-15 10:59:21 CMG Hausa

Asusun Bill da Melinda Gates ya kaddamar da rahoto a kwanakin nan cewa, kamata ya yi kasashen duniya su yayata matakai guda 7 da ake gudanarwa da kuma sabuntawa dangane da kiwon lafiyar masu juna biyu da iyaye mata da jarirai sabbin haihuwa a sassa daban daban na duniya. Idan wadanda suke matukar bukata sun ci gajiyar matakan, to, za a kubutad da masu juna biyu da iyaye mata da jariransu miliyan 2 ya zuwa shekarar 2030.

Rahoton ya yi karin bayani da cewa, tun daga shekarar 2016 har zuwa yanzu, an dakatar da aikin rage yawan mace-macen mata masu juna biyu da iyaye mata sanadiyar haihu ba da dadewa ba a duk fadin duniya, har ma a kasar Amurka da wasu kasashe, yawan mata masu juna biyu da iyaye mata dake mutuwa sanadiyar haihuwa yana karuwa. Yanzu a ko wace rana mata kusan 800 ne suke rasa rayukansu sanadiyar haihu a duniya. Ko da yake tun daga tsakiyar shekarun 2010 har zuwa yanzu, yara ‘yan kasa da shekaru 5 dake mutuwa ya ragu, amma jarirai sabbin haihuwa sun fi fuskantar hadarin mutuwa a wata na farko bayan haihuwa. Yawan mutuwar jarirai sabbin haihuwa ya kai kusan rabin mutuwar ‘yan kasa da shekaru 5 a duniya. An yi kiyasin cewa, kashi 74 cikin 100 na kananan yara ne suka mutu a cikin shekara ta farko bayan haihuwarsu.

Matakai 7 na inganta lafiyar masu juna biyu da iyaye mata da jariransu da muka ambato a baya, su ne da farko daukar cikakkun matakan shawo kan zubar jini da mata suke samu bayan haihuwa. Na biyu, kara kwayar bifidobacterium cikin nonon iyaye mata, a kokarin samar wa jarirai isasshen abubuwa masu gina jiki. Na uku, kara wa masu juna biyu abubuwa masu gina jiki iri daban daban, a kokarin rage yawan mutuwar jarirai. Na hudu, yi wa masu juna biyu da suke bukatar allurar iron preparation, don kare su daga matsalar karancin sinadarin Hb a cikin jini. Na biyar, yi wa masu juna biyu da ke fuskantar haihuwa kafin lokacin da aka tsara allurar maganin corticosteroids kafin haihuwa don kara karfin  huhun ‘yan tayi suke girma cikin sauri. Na shida, yi wa masu juna biyu allurar maganin azithromycin don rage kamuwa da kwayoyin cuta, ko ma kwayoyin cuta sun shiga jikinsu a lokacin samun ciki. Na karshe kuma, yin amfani da na’urorin zamani na tafi-da-gidanka wajen sa ido kan masu juna biyu wadanda suke fuskantar hadari, don daukar matakai kan lokaci. Ma’aikatan jinya da Ngozoma da ma’aikatan unguwa masu kula da haihuwa su ne suke gudanar da wadannan ayyuka.

Rahoton ya yi kira ga kasashen duniya da su dauki matakai nan da nan, don rage yawan mutuwar mata masu juna biyu da iyaye mata da jariransu, a kokarin ganin yawan mutuwar masu juna biyu da iyaye mata da suka haihu ba da dadewa ba zai wuce 70 cikin ko wadanne dubu 100 ba, kana yawan mutuwar jarirai sabbin haihuwa ba zai wuce 12 cikin ko wadanne 1000 ba a duniya. (Tasallah Yuan)