logo

HAUSA

Wakilin MDD ya bayyana fatansa game da samun zaman lafiya a Sudan

2024-01-15 11:40:15 CMG Hausa

Wakilin babban sakataren MDD a Sudan, Ramtane Lamamra ya bayyana fatansa game da yiwuwar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da ma kawo karshen rikicin kasar Sudan.

Lamamra ya bayyana hakan ne, a lokacin da yake ganawa da shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Sudan, kana babban kwamandan rundunar sojojin kasar Sudan (SAF) Abdel Fattah Al-Burhan, a birnin Port Sudan.

Jami’in na MDD ya ce, a ziyarar da ya kai kasar Sudan, ya yi shawarwari tare da jami'ai da wakilan kungiyoyin fararen hula da dama, inda ya sha alwashin yin aiki tare da dukkan bangarori, domin jaddada rawar da MDD ke takawa.

A nasa jawabin, Al-Burhan ya yi wa wakilin MDD bayani, kan kokarin neman mafita cikin lumana, yana mai jaddada kudurin gwamnatin Sudan, na kawo sauyi na demokuradiyya da kuma lokacin rikon kwarya da zai kawo karshe da shirya babban zabe.(Ibrahim)