logo

HAUSA

Jakadan Sin a Nijar ya gana da shugaban gwamnatin sojan kasar

2024-01-15 10:35:18 CMG Hausa

A ranar Asabar da ta gabata, Jiang Feng, jakadan kasar Sin a jamhuriyar Nijar ya gana da Abdourahamane Tchiani, shugaban gwamnatin sojan kasar ta Nijar.

Yayin ganawarsu, jakada Jiang ya ce, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba bayyana yanayin da ake fuskanta a fannin aikin hulda da sauran kasashe gami da nauyin da ya kamata a sauke, a wajen wani taron da ya gudana a birnin Beijing na kasar Sin, a watan da ya gabata, dangane da aikin hulda da kasashe daban daban. Inda shugaban kasar Sin ya ce, kasar Sin na ta kokarin sa kaimi ga kafa wata al'ummar bil Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya, da aiwatar da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya". Bisa wannan tunani ne, jakadan Sin ya ce Sin na son karfafa hadin gwiwa tare da Nijar, don raya tsarin kasancewar bangarori masu fada a ji sosai a duniya, da neman samun dunkulewar tattalin arzikin duniya wadda za ta amfanar da mabambantan kasashe.

A nasa bangare, Malam Tchiani ya yabi huldar dake tsakanin Nijar da Sin, da darajanta tunanin al'ummar bil Adam mai makomar bai daya, da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" da kasar Sin ta gabatar. Kana ya gode ma kasar Sin kan goyon bayan da ta nuna ma Nijar, da bayyana amincewarsa kan cewar, hadin gwiwar bangarorin biyu za ta haifar da dimbin nasarori, tare da samar da gudunmawa ga aikin raya al'ummar bil Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya a duniya. (Bello Wang)