Kungiyar Houthi: Jiragen leken asiri na Amurka da Birtaniya sun yi shawagi na tsawon sa’o’i a Hodeidah
2024-01-14 17:15:46 CMG Hausa
Ali Ahmed Kashar, Jami’in kungiyar Houthi, ya ce jirage marasa matuka na leken asiri mallakar Amurka da Birtaniya, sun shafe tsawon sa’o’i suna shawagi a birnin Hodeidah mai tashar ruwa na kasar Yemen, wato inda aka samu wasu sabbin rahotanni masu cin karo da juna game da zargin hare-hare ta sama.
Ali Ahmed Kashar, wanda shi ne mataimakin gwamnan yankin Hodeida, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, mambobin kungiyar sun ga jirage marasa matuka na leken asiri na shawagi a sararin samaniyar birnin a jiya tun daga safe har zuwa yamma. Ya kuma yi watsi da rahotannin da kafafen yada labarai na cikin da wajen kasar ke yadawa game da sabbin hare-hare ta sama kan sansanonin Houthi a Hodeidah.
Da farko, kafafen yada labarai sun ce jiragen saman kawance da Amurka ke jagoranta, sun kai hari wani sansanin sojin ruwa dake kusa da tashar jiragen ruwa. Mazauna wurin sun ce sun ji karar fashewar abubuwa da jiniyar motar daukar marasa lafiya, kana an baza mayakan Houthi a kewayen wurin da fashewar ta auku.
A jiya Asabar, manzon musammam na MDD a Yemen, Hans Grundberg, ya bukaci bangarori masu rikici su kai zuciya nesa yayin da ake fsukantar barazanar karuwar zaman dar-dar a yankin. (Fa’iza Mustapha)