logo

HAUSA

Cote d’Ivoire ta lallasa Guinea-Bissau a wasa na farko na gasar cin kofin nahiyar Afrika

2024-01-14 17:12:37 CMG Hausa

Kasar Cote d’Ivoire ta doke Guninea Bissau da ci 2-0, a wasan farko na gasar cin kofin nahiyar Afrika da ya gudana jiya Asabar a filin wasa na Alassane Ouattara dake birnin Abidjan na Cote d’Ivoire.

Dan wasan kasar Seko Fofana ne ya ci kwallo na farko bayan fara wasan da minti 5, inda Jean Phillippe Krasso ya zura kwallo na biyu a minti 59 da fara wasan.

Cote d’Ivoire na buga wasa ne a rukunin A tare da kasashen Nijeriya da Guinea Bissau da Equatorial Guinea. Kasashe biyu mafiya zura kwallo daga cikinsu ne za su cancanci shiga zagaye na biyu na qasar.

A jiya Asabar ne aka kaddamar da gasar cin kofin nahiyar Afrika karo na 34 a Abidjan, babban birnin harkokin tattalin arziki na kasar Cote d’Ivore.

Za a shafe kusan wata guda a na fafatawa a gasar wadda za ta gudana a filayen wasa 6 dake birane 5 na Cote d’Ivore. Kamfanonin kasar Sin ne suka gina wasu daga cikin filayen wasan da suka hada da na Alassane Ouattara da na Korhogo da na San Pedro.

Za a buga wasan karshe na gasar ne a ranar 11 ga watan Fabreru a birnin Abidjan. (Fa’iza Mustapha)