logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta fara aikin kawar da dazukan da suka zama maboyar ’yan ta’adda

2024-01-14 15:30:14 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar da aniyarta na sake tsari tare da kyautata sha’anin tsaro a dazukan dake kasar musamman wadanda yanzu haka suka kasance mafaka ga ’yan ta’adda.

Ministan muhalli na kasar Alh Balarabe Lawal ne ya tabbatar da hakan a garin Kaduna yayin wani taron karawa juna sani da aka shiryawa manyan jami’an ma’aikatar.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. //////

Taron wanda aka yi wa taken tsare-tsaren manufofi a kan mafiya fifikon muradun gudanar da harkokin muhalli na kasa.

Ministan muhallin ya ce, abun takaici yanzu dazukan Najeriya sun kasance sansanin ’yan ta’adda da mafarauta da kuma masu garkuwa da mutane. Hakan kamar yadda ya ce yana matukar haifar da tafiyar hawainiya wajen samun nasarar shirin gwamnati wajen shawo kan matsalolin zaizaiyar kasa da kwararowar Hamada.

A sakamakon wadannan jerin kalubale, yanzu gwamnati bisa samun hadin gwiwar shugaban kasa na daukar matakan samar da jami’an tsaron daji da za su fatattaki irin wadannan bata garin mutane, kuma za a samu nasarar hakan ne da taimakon kungiyoyin kasa da kasa.

Ya ce sare irin wadannan dazuka shi ne mataki na karshe da za a iya dauka idan har sauran matakan da aka dauka ba su yi tasirin-a-zo-a-gani ba.

“Idan har aka sare dazukan, an tozartar al’ummomin da suke zaune a yankunan da dazukan suke, sannan kuma sannu a hankali kasar za ta fuskanci matsalolin gurbatar yanayi da makamatansu.” (Garba Abdullahi Bagwai)