logo

HAUSA

Sin: Matakan soji da Amurka da Birtaniya suka dauka kan mayakan Houthi a Yemen ba za su cimma burin da ake fata ba

2024-01-13 20:29:36 CMG Hausa

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya ce matakan soji da Amurka da Birtaniya suka dauka kan kungiyar Houthi a Yemen, ba za su cimma burin da ake ikirari ba.

Zhang Jun ya bayyana haka ne jiya Juma’a, yayin wata zama ta gaggawa da Kwamitin Sulhu na MDD ya kira, dangane da yanayin da ake ciki a yankin Jan Teku.

Ya ce mayakan Houthi sun shafe wani lokaci suna kai hare-hare a kai a kai kan jiragen ruwan kasuwanci a tekun, lamarin dake yin tsaiko ga tsarin cinikayya na duniya. Ya kara da cewa, kasar Sin ta sha nanata kira ga mayakan kungiyar Houthi su dakatar da kai hare-hare kan jiragen. Haka kuma, tana kira ga dukkan bangarori, musammam manyan kasashe, su taka rawar da ta dace cikin hadin gwiwa, domin kare yankin ruwan Jan Teku.

A cewar Zhang Jun, kasar Sin na takaicin ganin yadda matakan soji da aka dauka kan Yemen ba su tsaya kadai ga lalata ababen more rayuwa ba, har ma da jikkatar fararen hula da tsananta barazanar tsaro a ruwan, wanda bai dace da kare tsaro da ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwan kasuwanci ba. Ya ce matakan soji za su iya kara yin mummunan tasiri kan yanayin siyasar Yemen, yana mai cewa, babu yadda za a yi irin wadannan matakai su kai ga cimma burikan da ake so.

Har ila yau, wakilin na Sin ya ce kasarsa na gargadin cewa, yankin Gabas ta Tsakiya na gab da fadawa mummunan hadari. Kuma abu mafi muhimmanci shi ne kai zuciya nesa domin kaucewa ta’azzarar rikicin. (Fa’iza Mustapha)