logo

HAUSA

Gwamnatin Zimbabwe ta yabawa ci gaban da ake samu a masana'antar samar da karafa da Sin ta zubawa jari

2024-01-13 16:40:55 CMG Hausa

Ministan kula da harkokin masana'antu da cinikayya na kasar Zimbabwe, Sithembiso Nyoni, ya yabawa ci gaban da kasar take samu wajen kafa masana'antar samar da karafa mafi girma a kasar, a yankin Manhize na gundumar Chirumhanzu dake lardin Midlands.

Ministan ya bayyana haka ne a jiya, yayin rangadin da ya kai masana'antar da ake gab da kammala aikinta, yana mai cewa, masana'antar ta zamani ba samar da ingantattun kayayyakin karafa kadai za ta yi ba, har ma da bayar da gagarumar gudunmuwa ga habakar tattalin arzikin kasar.

Kamfanin Tsingshan na kasar Sin ne ke gudanar da aikin ta hannun reshensa wato kamfanin tama da karafa na Dinson. Ana sa ran masana'antar za ta kai Zimbabwe matsayin mai samar da karafa mafi girma a shiyyar.

Har ila yau, ministan ya bayyana cewa, idan ta fara aiki gadan-gadan, masana'antar wadda daya ce daga cikin mafi samun jarin bangarori masu zaman kansu a kasar, za ta samar da guraben ayyukan yi na kai tsaye da ma wadanda ba na kai tsaye ba, da dama. (Fa'iza Mustapha)