Za ta kashe dala miliyan 156 wajen aikin inganta layukan dakon wuta daga Najeriya zuwa kasashe 4 makwabta
2024-01-13 15:56:57 CMG HAUSA
Hukumar bunkasa harkokin samar da wutar lantarki tare da cinikinsa a tsakanin kasashen dake kungiyar Ecowas WAPP ta kebe dala miliyan 156 a kasafin kudinta na wannan shekara wajen ci gaba da aiwatar da aikin samar da layin dakon wuta mai karfin KV 320 da zai tashi daga Najeriya zuwa Janhuriyar Nijar, da Benin da Burkina Fasso da kuma Togo.
Hukumar ta tabbatar da hakan ne jiya Juma’a 12 ga wata a birnin Abuja yayin taro karo na 7 na kwamitin sanya ido kan aikin wanda zai kai tsawon kilomita 913.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.