logo

HAUSA

An bude gadar da kasar Sin ta gina a birnin Abidjan a hukumance

2024-01-12 09:48:56 CMG Hausa

A ranar Alhamis ne aka bude wata gada da kamfanin gine-gine na kasar Sin ya gina a hukumance, wanda za ta rage cunkoso a titunan Abidjan, yayin da dubban dubatar masoya kwallon kafa daga sassan duniya ke zuwa kasar domin halartar gasar cin kofin nahiyar Afirka karo na 34. 

A ranar Laraba ne firaministan kasar Cote d’Ivoire Robert Beugre Mambe ya duba ingancin gadar, inda ya taya murnar kammala aikin tare da gaisawa da ma'aikatan daga kasar Sin da kuma kasar ta yammacin Afirka. Ya bayyana aikin gadar a matsayin wani muhimmin shiri na samar da ababen more rayuwa, wanda ya zama muhimmin hanyar sufuri don kyautata zirga-zirga a babban birnin kasar Abidjan.

Gadar da ke yammacin birnin Abidjan mai tsawon kimanin kilomita 7, an bude ta kwanaki biyu gabanin gasar cin kofin nahiyar Afirka karo na 34, wanda zai gudana har zuwa ranar 11 ga watan Fabrairu. (Muhammed Yahaya)