Sojojin Najeriya sun kashe ’yan bindiga 86 a wani samame
2024-01-12 11:13:17 CMG Hausa
Sojojin gwamnatin Najeriya sun kashe a kalla mutane 86 da ake zargin ’yan bindiga ne tare da tsare wasu 101 a wasu hare-hare a fadin kasar a cikin makon da ya gabata, kamar yadda rundunar sojin kasar ta sanar a jiya Alhamis.
Edward Buba, kakakin rundunar sojin Najeriya, ya shaidawa manema labarai a babban birnin tarayya Abuja cewa, farmakin da sojojin suka gudanar ya mayar da hankali ne kan fatattakar sansanonin ’yan ta'adda daga sama, sannan kuma sun ba da karfi sosai a yankunan da ’yan ta'addan ke fakewa.
Buba ya ce rundunar sojin sun kuma sako wasu da dama da aka yi garkuwa da su. (Muhammed Yahaya)