logo

HAUSA

Gungun ’yan ta’adda sun kai hari kan wani kauyen jihar Katsina

2024-01-12 09:31:40 CMG Hausa

Wasu gungun ’yan ta’adda sun kai hari kauyen Kukar-Babangida dake yankin karamar hukumar Jibiya a jihar Katsina, inda nan take suka hallaka mutane 10 ciki har da dagacin kauyen Mal. Maigari Haruna.

Da misali karfe 1 da rabi na daren ranar Alhamis, 11 ga wata ne ’yan ta’addan suka shiga cikin kauyen a kan babura dauke da muggan makamai, inda suka yi tabi gida-gida suna cin zarafin mutane tare da kwace masu kayyyaki kafin daga bisani su harbe wadanann mutane 10.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahato. 

ASP Abubakar Aliyu shi ne kakakin rundunar ’yan sandan jihar ta Katsina ya kuma tabbatar da faruwar wannan hari, “Mun samu rahoton wasu bata garin mutane dauke da muggan makamai da suka hadar da bindiga kirar AK47, inda suka kai hari wani kauye da ake kira Kukar-Babangida, kuma sanadiyar wannan hari nasu kimanin mutane 9 suka rasa ransu tare da kona motoci kimanin 5. Da samun wannan rahoto ba tare da bata lokaci ba, baturen ’yan sanda dake wannan yanki na Jibiya ya garzaya yankin da aka kai harin domin kai dauki. A halin da ake ciki, jami’an ’yan sanda suna nan sun bazama cikin dajin dake makftaka da yankin na Jibiya domin tabbatar da ganin an samu nasarar kamo wadanda suke da hannu wajen wannan aika-akai domin tabbatar da ganin an gurfanar da su gaban kotu don su fuskanci hukunci a bisa abun da suka aikata.”(Garba Abdullahi Bagwai)