logo

HAUSA

Dakarun Houthi: Amurka da Birtaniya sun kai harin sama a Yemen

2024-01-12 14:02:23 CMG Hausa

 

Kamfanin dillancin labaru na Saba na kasar Yemen ya ruwaito yau Jumma’a cewa, da sanyin safiyar yau ne jiragen saman yakin kasashen Amurka da Birtaniya, suka kai hari ta sama kan birnin Sanaa, fadar mulkin kasar, da birnin Hodeidah da ke gabar tekun Maliya dake yammacin kasar, da kuma wasu wuraren a lardin Saada da ke arewacin kasar.

Kafofin yada labarun Amurka sun tabbatar da labarin.

Sai dai kuma dakarun Houthi sun bayyana yau cewa, hare-hare ta sama da Amurka da Birtaniya suka kai a birnin Sanaa, fadar mulkin kasar da wasu wurare, kutsa kai ne da suka yi wa Yemen. Kasashen 2 za su girbi sakamakon mummunan abin da suka aikata. (Tasallah Yuan)