logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Da Su Goyi Bayan Kasashen Yammacin Afirka Da Na Sahel

2024-01-12 12:21:35 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Dai Bing ya yi kira ga kasashen duniya da su goyi bayan kasashen yammacin Afirka da na Sahel a fannoni da dama.

Dai ya bayyana haka ne jiya Alhamis a yayin da aka dudduba batun kasashen yammacin Afirka da na Sahel a kwamitin sulhu. Ya kara da cewa, tun daga shekarar bara, kasashen sun yi kokari sosai wajen shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Amma ana fuskantar matsaloli da kalubaloli a yankin. Ba a samu kwanciyar hankali a wasu kasashe ba, inda kuma ake samun sabani tsakanin al’umma. Wajibi ne kasashen duniya su mara wa kasashen baya wajen zabar hanyar raya kasa bisa yanayin da suke ciki. Yadda aka tilasta musu tafiyar da harkoki ta hanyar da ba ta dace ba, da kuma yi musu gyare-gyare bisa sunan demokuradiyya, ba sa daidaita matsalolin da suka haifar da rashin kwanciyar hankali a wadannan kasashe, har ma sun haddasa sabbin rudani.

Dai ya ci gaba da cewa, har kullum kasar Sin na mara wa kasashen yammacin Afirka da na Sahel baya wajen inganta kwarewarsu bisa tsarin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC da shawarar Raya Duniya, a kokarin samun ci gaba mai kunshe da kowa kuma mai dorewa, da aza harsashin samun dauwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a kan lokaci. Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi zai ziyarci kasashen Togo da Kodivwa da ke yankin a mako mai zuwa, ziyarar da ta zama ta 34 da ministan harkokin wajen kasar Sin ta yi a farkon ko wace shekara kafin ziyartar sauran kasashe a cikin shekaru 34 a jere da suka gabata, kana za ta ba da gudummowar Sin wajen sa kaimi kan samun zaman lafiya da ci gaba a yankin. (Tasallah Yuan)