logo

HAUSA

Shugaban kasar Masar Sisi ya gana da Blinken domin tattauna halin da yankin gabas ta tsakiya ke ciki

2024-01-12 11:34:13 CMG Hausa

Shugaban kasar Masar Sisi ya gana da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Blinken a babban birni Alkahira a ranar 11 ga wata, inda suka tattauna batutuwa game da halin da yankin gabas ta tsakiya ke ciki, musamman batun yankin Palestine da rikicin zirin Gaza da kuma sauran batutuwa.

Fadar shugaban kasar Masar ta sanar da cewa, Sisi ya gabatar wa Blinken irin kokarin da kasarsa ke yi na mu’amala da bangarori daban-daban, wajen tabbatar da tsagaita bude wuta a Gaza, da kuma kawo isassun kayayyakin agajin jin kai cikin zirin Gaza.

A nasa bangaren kuma, Blinken ya ce Amurka ta yaba wa kokarin da Masar ta yi don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Har wa yau, bangarorin biyu sun nuna adawa ga yunkurin da ake yi na raba Falasdinawa da kasarsu. Sun kuma yi alkawari cewa tsarin kafa kasashe biyu zai zama babban tushen tabbatar da zaman lafiya. (Hamza Wang)