logo

HAUSA

Manyan abubuwan da suka faru a fannin wasanni a shekarar 2023

2024-01-11 20:39:25 CMG Hausa


Ga wasu daga cikin zababbun labaran wasanni da suka yi fice a shekarar 2023, wadanda kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya tattara:

QIN HAIYANG YA LASHE KAMBI 3 A GASAR LINKAYA

Dan wasan linkaya na Sin Qin Haiyang, ya baiwa duniya mamaki, bayan da ya yi nasarar lashe kambin linkaya 3 a watan Yulin shekarar da ta shude a Fukuoka. Qin ya lashe tseren linkaya na mita 200 a gasar kasa da kasa da ta gabata. Kaza lika, ya lashe gasar linkaya ta mita 50 da mita 100, wanda hakan ya sanya shi zama dan wasan linkaya na farko da ya taba lashe lambobin zinari 3 a gasar kasa da kasa guda daya.

Qin ya ce "Dama na bayyana buri ne, wato lashe gasannin 3. Na san ba wanda ya taba lashe lambobin zinarin 3 kafin yanzu, amma ina da kwarin gwiwar yin iyakacin kokari na."

A ajin mata ‘yan wasan linkaya kuwa, Kaylee McKeown daga Australia, ta yi nasarar lashe gasar mita 50, da mita 100 da mita 200 salon “backstroke”. Kafin McKeown, ba wata mace da ta taba lashe zinari a gasar mita 50 da mita 100 a gasar kasa da kasa daya, ballantana lambar zinari 3 a lokaci guda.

Jadawalin ‘yan wasa mafiya hazaka na 2023 ba zai cika ba, har sai an anbaci dan wasan linkaya na Faransa Leon Marchand, wanda ya karya matsayin bajimtar Michael Phelps, a gasar linkaya ajin maza ta daidaikun ‘yan wasa ta mita 400. Leon Marchand ya karya matsayin bajimtar gasar da aka kafa shekaru 15 da suka gabata.

FEMKE TA FARFADO BAYAN CIN KARO DA RASHIN NASARA

‘Yar wasan tsere Femke Bol daga kasar Netherlands, ta yi rawar gani a gasar wasannin motsa jiki ta kasa da kasa da ta gudana a Budapest, bayan ta fara gasar da rashin nasara a gudun mita 400 na ‘yan wasa 4. Bayan mako guda da faduwar ta a kusa da layin karshe na gudun mita 400, Bol ta farfado, inda ta lashe tsere da tsallake shingaye na mita 400.

A cewar Femke Bol "Ba abu ne mai sauki na manta da abun da ya faru a tseren ‘yan wasa 4 da muka shiga ba, amma duk da haka, sauran ‘yan wasan mu sun kasance tare da ni, sun kuma kwantar mun da hankali".

Baya ga tsere da tsallake shingaye na mita 400, Bol ta kuma doke Nicole Yeargin ta Birtaniya, da Stacey Ann Williams ta Jamaica, a gudun mita 50, wanda ya ba ta damar lashe zinari na biyu a gasar ta Budapest.

GASAR WASANNI TA ASIYA TA FITO DA MANUFAR MARTABA JUNA DA ABOTA

Daya daga muhimman gasanni da suka wakana a shekarar 2023 da ba za a manta da su ba, ita ce gasar wasanni ta Asiya da ta gudana a birnin Hangzhou na kasar Sin, inda a lokacin ‘yar wasan linkaya ta Sin Zhang Yufei, ta yi nasara kan abokan fafatawar ta Yu Yiting ta Sin da Rikako Ikee ta Japan.

Da wannan nasara, Zhang ta lashe lambar zinari ta 6 a gasar linkaya, inda ya kammala karo na 6, da linkayar mita 50 salon “butterfly” bayan wuce Yu Yiting da Ikee.

Duk da nasarar da Zhang ta samu, ita ma ‘yar wasar Japan Rikako Ikee, wadda ta lashe lambar tagulla a matsayi na 3 ta yi rawar gani, duba da cewa wannan ne karo na farko da ta shiga gasar kasa da kasa, tun bayan da aka tabbatar da ta kamu da cutar sankarar jini a watan Fabarairun shekarar 2019.

Yayin da suka hau dandamalin karbar lambobin yabon da suka lashe, Zhang ta ce "Na sa a rai na ba zan yi kuka ba, amma lokacin da aka kira sunan Ikee sai na ji hawaye suna kokarin zubo min. Amma na yi tunanin dukkanin kyamarori suna kallon mu, ba zan yi kuka ba. Sai dai lokacin da na ga ta rungume kocin ta tana zubar da hawaye, sai na ji ba zan iya daurewa ba, sai na fara kuka".

Zhang tare da abokin linkayata Qin Haiyang, wanda ya lashe lambobin zinari har 5 a gasar ta Hangzhou, sun shiga tarihi na ‘yan wasa tare, mafiya kwarewa a gasar ta Asiya ajin linkaya salon “breaststroke”.

A bangaren ta, ‘yar wasan linkaya ta Japan Ikee, wadda ta samu nasarar lashe lambar karramawa ta ‘yan wasa mafiya hazaka a gasar Asiya ta 2018, bayan ta lashe lambobin zinari 6, da na azurfa 2, a wannan karo ta taya Zhang murna tare da yaba mata.

A cewar Ikee "Zhang na da hazakar linkaya a duk lokacin da ake gudanar da gasa. A gani na ba ta da abun da zai tsayar da ita, tana sa ni jin karin karsashi, ganin yadda wata ‘yar wasan linkaya ta Asiya ke nuna bajimta. Ina fatan kamo ta a fannin kwazo".

MANCHESTER CITY TA LASHE GASAR CHAMPIONS LEAGUE

Wani abun faranta rai ga magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, shi ne yadda kungiyar ta su lashe gasar zakarun turai ta UEFA Champions League, a karon farko bayan ta doke Inter Milan a wasan karshe da suka buga a filin wasa na Ataturk dake Istanbul.

Dan wasan tsakiya daga Sifaniya Rodri ne ya jefa kwallo daya tilo da aka ci a wasan karshe na gasar, a minti na 68 da take wasa, wanda hakan ya jefa ‘yan wasa, da jami’ai, da magoya bayan kungiyar Manchester City cikin farin ciki, da murnar nasarar da suka samu.

Yanzu dai ‘yan wasan kungiyar Manchester City karkashin koci Pep Guardiola, sun cimma nasarar da suka jima suna nema, kuma kungiyar ta zamo ta biyu cikin jerin kulaflikan dake buga gasar Firimiyar Ingila, da ta taba lashe kofuna 3 a kakar wasa daya, wato gasar Firimiya, da FA Cup, da kuma kofin zakarun turai na European champions. Kafin wannan lokaci, abokiyar hamayyar ta Manchester United ta kafa irin wannan tarihi a shekarar 1999.

Koci Guardiola, ya cika da farin ciki bayan kammala wasan na karshe, inda ya ce "Wannan kofi ne mai wahalar lashewa. Wannan nasara ta shiga cikin taurari. Kofin ya zama na mu".

CARMONA TA CI KARO DA NASARA DA BAKIN CIKI A LOKACI GUDA

‘Yan wasan kwallon kafa na kasar Sifaniya sun yi nasarar lashe kofin kwallon kafa na duniya a shekarar 2023 a karo na farko, bayan sun doke abokan fafatawar sun a Ingila da ci daya da nema, gaban ‘yan kallo sama da 75,000, a wasan da aka buga a filin wasa na Sydneyn kasar Australia.

‘Yar wasan Real Madrid Olga Carmona, wadda ta ciwa kasar Sifaniya kwallo daya tilo da aka ci a wasan na karshe ana cikin minti na 29, daga bisa ni ta samu labarin rasuwar mahaifin ta, wanda ya jima yana fama da jinya.

Cikin wani sako da ta wallafa a shafin ta na yanar gizo, ta ce "Na san ka karfafa min gwiwa wajen cimma wani buri na musamman. Baba na san kana kallo na a daren nan, kuma ka yi alfahari da ni".

Bisa alkaluman da aka fitar, ‘yan kallo 1,978,274 ne suka kalli wasanni a gasar da aka buga a filayen wasa 10 dake Australia, da New Zealand, tsakanin ranaikun 20 ga watan Yuli zuwa 20 ga watan Agusta, wanda hakan ya zarce adadin wadanda suka kalli gasar ta shekarar 2015 a kasar Canada, wato ‘yan kallo 1,353,506 da suka kalli wasanni 52.

AUSTRALIA TA LASHE KOFIN DUNIYA NA GASAR CRICKET A KARO NA 6

Kafin kammala gasar kwallon gora ta Cricket, wadda aka buga wasan karshenta a filin wasa na Narendra Modi dake Ahmedabad, da yawa daga masu fashin baki game da gasar ba su yi tsammanin kasar Australia za ta iya lashe kofin na shekarar 2023 ba. Musamman ganin yadda kasar ta yi rashin nasara a wasanni 2 na farkon gasar da ta buga da India da Afirka ta kudu.

To sai dai kuma, karkashin zaburarwar kyaftin din kungiyar ta Australia wato Pat Cummins, kungiyar ta lashe wasanni 9 a jere, bayan biyun farko da ta yi rashin nasarar su. Cikin wasannin da Australia ta lashe har da wasan karshe da mai masaukin bakin gasar wato Indiya.

An bayyana dan wasan Australia Travis Head, a matsayin ginshikin nasarar kungiyarsa, inda ya yi matukar bayar da gudummawa da ta kaiwa ga nasarar Australia, wadda ta dauki kofin Cricket na duniya a karo na 6.

An dai gudanar da wasan karshe na gasar Cricket ta kasa da kasa ne gaban ‘yan kallo sama da 100,000. Kuma nasarar da Australia ta samu ta kawo karshen tarin nasarori da ajin maza na wasan Cricket na kasar ya samu a shekarar ta 2023, bayan da kungiyar ta yi nasarar lashe kofin duniya na “World Test Championship”, da kofin “Ashes” da aka buga a kasar Ingila.

DJOKOVIC YA CI GABA DA KARE KAMBIN BAJIMTA A WASAN TENNIS

Zakaran wasan tennis dan asalin kasar Serbia Novak Djokovic, ya ci gaba da kare matsayin bajimtarsa a shekarar 2023. Inda a watan Yuni ya doke Casper Ruud a wasan karshe na gasar “French Open”, ya kuma sha gaban Rafael Nadal a matsayin dan wasan tennis ajin maza na farko da ya lashe kofin Grand Slam har sau 23.

Novak Djokovic mai shekaru 36 a duniya, ya ci gaba da kare tarihin da ya kafa, watanni 3 bayan nasarar sa a “French Open”, lokacin da ya doke Daniil Medvedev a gasar “US Open” a karo na 4, kuma da wannan kofi ya kafa tarihin dan wasa da ya lashe “Grand Slam” na daidaikun ‘yan wasa a budadden filin wasa har karo 24.

Djokovic dai ya kammala shekarar 2023 da kofuna 7 a gasanni 12 da ya halarta, ciki har da na manyan gasannin “Grand Slam” guda 3.

Da yake tsokaci game da nasarorin da ya samu, Djokovic ya ce "Duk da cewa na lashe “Grand Slam” guda 3 cikin 4 da na buga, kana na buga wasannin karshe 4, wannan ba ita ce shekarar da na fi samun nasarori ba, amma abun farin ciki ne ganin na kai ga wannan matsayi".

AFIRKA TA KUDU TA ZAMO ZAKARAR WASAN RUGBY

Kasar Afirka ta kudu, ta ci gaba da kare kambin ta na wadda ta fi ko wacce kasa samun nasara a wasan rugby, bayan da a shekarar 2023 ta lashe gasar rugby ta duniya a karo na 4.

Nasarar da kasar ta samu a gasar da aka buga a Faransa, ta wanzar da jerin nasarorin ta a wasan, duk da cewa masharhanta da dama ba su yi tsammanin za ta kai ga nasarar lashe kofin na Faransa ba. Musamman dubu da cewa, akwai tarin ‘yan wasan kasar kwararru da suka yi ritaya, kana kungiyar kasar ta rasa karfin hadin kan ‘yan wasa.

Kafin gasar ta Farasan, kasashen Ireland, da Faransa, na gaban Afirka ta kudu a jerin kasashe mafiya kwarewar wasan na rugby, yayin da aka rika hasashen kungiyar New Zealand, wadda ta sha daukar kofin gasar za ta iya lashe gasar ta Faransa. To sai dai hakan ba ta faru ba, domin kuwa a wasan karshe da aka fafata a filin wasa na Stade de France, Afirka ta kudu ta doke New Zealand da ci 12 da 11.

Game da nasarar da suka samu, kyaftin din Afirka ta kudu Siya Kolisi ya ce "Wannan ba batu ne na mu ‘yan wasa ba, nasara ce ga daukacin al’ummar Afirka ta kudu, kuma mun nunawa duniya abun da za mu iya yi da wadannan tarin ‘yan wasa na mu".